Wata babbar ambaliyar ruwa a yankin Black Sea ta Arewacin Turkiyya ta kashe mutane hudu, da suka hada da soja guda, yayin da wasu 11 suka bata, in ji Ministan cikin gida Suleyman Soylu a ranar Lahadin, 23 ga Agusta, yayin da hukumomi ke gudanar da aikin tsaftacewa da ceton mutane.