Joe Biden, ya bayyana kafa babban tarihi, a yayin da yake gabatar da Sanata Kamala Harris, wadda ya zaba a zaman mataimakiyarsa a gangamin yakin neman zabe.
Biden da Harris da dukan su suke sanye da takunkumin rufe fuska sakamakon annobar coronavirus, sun yi jawabai a dandalin wani taro.