Shugaban kungiyar kasashen yankin Amurka ta Kudu da ake cewa OAS a takaice sun gana da tsohon mai gabatar da kara na kotun manyan laifuka na kasa da kasa akan yiwuwar a tuhumi mahukuntar kasar ta Venezuela akan take hakkin bil-adama.
Cikin fushi shugaba Donald Trump na Amurka ya ci gaba da amfani da hanyar sadarwan nan da ya saba amfani da ita wato Twitter, domin caccakar wadanda yake kallo a matsayin makiyansa, ciki harda daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwarsa wato atoni janar na Amurka.
Hadakar kungiyoyin kare hakkin bil Adama ta koka game da halin ko in kula da shugabanin ke nunawa akan halin da yan gudun hijira na yankin Mambila a jihar Taraba suke ciki, musamman ta fuskar kiwon lafiya.
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya a yankin tabkin Chadi yayi kashedin cewar dubban mutane ka iya rasa rayuwansu saboda yunwa a yankin.
An fara aikin gina ganuwar jami’ar Maiduguri don hana masu kai harin kunar bakin wake a jami’ar kaiwa cikin harabar jami’ar. Hukumar jami’ar Maiduguri tana gina wannan ganuwar ce da taimakon gwamnatin jihar Borno.
Wata tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyara a karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna inda wasu yan pashi da makami suka kai hari a ranar sha bakwai ga wannan wata na Yuli.
A karo na biyu cikin mako guda wasu mahara sun kai hari a yankin Ngalewa dake Jamhuriyar Nijar, inda ake kyautata zaton cewa maharan 'yan kungiyar Boko Haram ne, inda akalla mutane tara suka mutu.
An fara taron kolin na kungiyar kasashen Afirka a karo na 29 a birnin Addis Ababa, inda shugabannin kasashe suka hallara domin tattauna matsalolin da ke addabar kasashen nahiyar.
Labarun da muka samu da dumi dumun su na cewa Korea ta arewa ta sake gwajin harba wani mamaki mai lizami a yau Talata. Rundunar Sojan Korea ta arewa ce ta bada wannan labari.
Amurkawa duk fadin kasar na bikin samun 'yancin kasar. Tun shekara 1941 aka fara kebe ranar 4 ga watan Yulin a matsayin ranar gudanar da shagulgulan wannan rana.
Shugabannin a Najeriya na ci gaba da yaba wa tare da mika ta'aziyyarsu bisa rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Dan Masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda ya rasu a farkon makon nan.
A yau Talata ake shirye-shiryen jana'izar tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Alhaji Yusuf Maitama Sule, a birnin Kano bayan rasuwarsa a kasar Masar a jiya Litinin inda ya yi wata 'yar karamar jinya.
Ana ci gaba da kai ruwa rana a Brazil, yayin da shugaban kasar Michel Temer ya yi kememe ya ce ba zai sauka akan karagar mulki ba, duk da cewa ana zarginsa da laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.
Ofishin kasafin kudin majalisar dokoki da bashi da alaka da banbancin siyasa, ya fitar da wata kididdiga wacce ta nuna cewa akalla Amurkawa miliyan 22 ake tunanin za su rasa inshorar lafiyarsu nan da wasu shekaru masu zuwa idan aka amince da sabon tsarin kiwon lafiya da zai maye gurbin Obamacare.
Firai ministar Birtaniya Theresa May, ta yi kokarin ba miliyoyin ‘yan kasashen Turai dake zama a kasar tabbacin cewa, rayuwarsu da ta iyalansu ba za ta sauya ba, bayan da kasar ta fara shirin ficewa daga kungiyar tarayyar Turai a 2019.
An sami gawar dan jaridar da ya bace a jihar Michoacan dake yammacin kasar Mexico, abinda ya kai bakwai, adadin ‘yan jarida da aka kashe a kasar bana.
Hukumomi a jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar sun tabbatar da kamewa da tsare wasu malaman makarantun boko na jabu arba’in da shida da ake zargi da laifin anfani da takardun jabu na kamala karatun jami’a.
Fannin noman albarkatun gonaki a Jihar Filato dake tsakiyar Najeriya, na fuskantar kalubale bayan da aka gano wata cuta dake barnata amfanin gona. Filato, jiha ce da ta yi fice a fannin noman kayan marmari da ma hatsi.
Iyalan Otto Warmbier, dalibin jami’a Ba’amurken nan da Koria ta Arewa ta tsare na kusan shekara daya da rabi sun sanar jiya Litinin cewa ya rasu.
Yan sanda sunce an kashe wani mutum bayanda ya rafka motarsa dake dankare da nakiya kan wata motar ‘yan sanda a kasuwar Champs Elysees dake samun cunkoson jama’a jiya Litinin.
Domin Kari