Tsohon shugaban hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin zagon kasa ta EFCC, Mallam Nuhu Ribadu ya dora muryarsa a kan na masu yi wa marigayi Dan Masanain Kano kyakkaywan shaida yana mai cewa, Maitama Sule dattijo ne kuma abin koyi.
Ribadu ya ce zama da Dan Masanin Kano tamkar zama a jami’a ce saboda "za ka samu karuwa ta musamman kan batutuwan siyasa."
Da yake ci gaba da yabawa marigayin, tsohon shugaban na EFCC ya ce a duk lokaci da aka hadu da Dan Masanin Kano za ka ji sabon abu da zai kara maka ilimi.
Saurari rahoton nan domin jin karin bayani.
Facebook Forum