Labarun da muka samu da dumi dumun su na cewa Korea ta arewa ta sake gwajin harba wani mamaki mai lizami a yau Talata. Rundunar Sojan Korea ta arewa ce ta bada wannan labari.
A can kasar Syria kuma rundunar sojan kasar ta ayyana tsagaita bude wuta a kudancin kasar har zuwa ranar Alhamis domin goyon bayan yunkuri sasantawa a kasar.
Jiya Litinin aka bada wannan sanarwar kwana daya kafin ayi shawarwarin samun zaman lafiya a Astana baban birnin kasar Kazakhstan.
Facebook Forum