Masu shigar da kara a Somalia sun tuhumci wasu mutane biyar da hannu a cikin wani harin bam da aka kai da wata babbar mota a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata a babban birnin kasar Mogadishu inda aka kashe mutane 512, harin ta’addanci mafi muni a tarihin nahiyar Afrika baki dayanta.
Rundunar sojan Najeriya tace sama da mutane 700 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa dasu sun arce daga inda ake tsare da su a yankin arewa maso gabashin kasar.
Jakadan Amurka a Najeriya Ambassador Stuart Symington ya mikawa babban hafsin hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marsha Sadik Abubakar takardan amincewar Amurka na sayarwa Najeriya manyan jiragen yaki samfurin A29 Super Tucano goma sha biyu.
Madugun yan adawan Rasha, Alexie Navalny ya nemi mutanen Rasha da su shirya gagarumar zanga zanga a duk fadin kasar a ranar 28 ga watan Janairu mai zuwa, domin bada goyon baya ga kauracewa zaben kasar mai zauwa.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fada a jiya Laraba cewa wani hari ta sama da aka kai a Somalia a jajibirin Krismeti ya kashe mayakan al-Shabab 13. Rundunar hadin gwiwan Amurka da Afrika tace gwamnatin Somalia ta timaka wurin shirya kai wannan farmakin a arewa maso yammacin Kismayo.
Al’ummar kasar Liberia na ci gaba da jiran sunan mutumen da zai zama sabon shugaban kasarsu a daidai lokacinda jami’an Hukumar zabe ke ci gaba da kirga kuri’un da aka jefa a zaben baya-bayan nan na raba gardama.
Wata kungiyar fafutukar zaman lafiya a jihar Kaduna ta Global Peace Foundation ta yi kira ga hukuma da gabatar da duk masu tada rikici a cikin jihar gaban shari’a saboda sauran jama'a su dauki darasi. Kungiyar tace rashin hukunta masu laifi zai ba mutane daman aikata son zuciya.
Mako guda bayan wani rikici da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a garin Ananku na jihar Anambara a Nigeria, mazauna yankin sun ce ana samun kwanciyar hankali kuma suna ci gaba harkokinsu na yau da kullum.
Wasu mahara a gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Congo sun kona gidan gona mallakar shugaban kasar, Joseph Kabila kurumus a jiya Litinin kuma suka kashe wani dan sanda.
A wata sabuwa kuma, mayakan al-Shabab na kasar Somalia sun zartar da hukuncin kisa a kan mutane biyar ciki har da wani matashi mai shekaru 16 da suke masa zargin dan leken asiri ne na kasashen Kenya da Amurka da kuma Somalia.
Sojojin Najeriya sun tarwatsa wani yunkurin kai harin ta’addanci da mayakan Boko Haram suka shirya kaiwa a Maiduguri a jiya Litinin, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba da ya kai su ga arcewa domin ceton rayuakansu.
Shugabannin addinin Krista a Najeriya sun nanata muhimmancin zaman lafiya da kuma aika sakon zaman lafiya da hadin kai tsakanin yan Najeriya. Manyan mabiya addinin Kristan sun yi wannan kira ne yayin da ake shirin buki Krismeti na wannan shekarar 2017.
Bayan kamala babban taron babban jami’iyar adawa a Najeriya ta PDP, wata kungiya ta kunno kai da take kiran kanta Fresh PDP wacce take kalubalantar babban taron da ya zabi sabon shugaban jami’iyar Uche Secondus.
Saudi Arabia tace zata bude tashar jiragen ruwa da yan tawayen Houthi na Yeman ke rike da shi domin shigar da kayan agaji na jin kai har tsawon kwanaki 30 duk da harin makami mai lizzami da yan tawayen suka kai a yankin Saudia.
Majalisar dokokin kasar Uganda ta kada da wata kuri’ar fidda kayade yawan shekaru ga masu shiga takarar shugabancin kasa da gagarumin rinjayi, domin bada dama ga daya daga cikin dadaddeun shugabannin Afrika ya ci gaba da mulki har izuwa shekarar 2031.
Kungiyoyin Musulmi karkashin leman hadakarsu ta Muslim Right Concern sun shirya taron manema labarai a kan kin rantsar da wata dilabar musulma a makarantar lauyoyi ta kasa a Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amshi sakamakon binciken komitin da ya kafa ya gudanar da bincike a kan makudan kudaden da aka gano a gidan tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa Ambassador Ayo Oke da suka kai dala miliyon 43.
Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya bayyana nadamarsa ga cijewar shirin shiga tsakanin bangarorin adawar Syria a Geneva da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a makon da ya gabata.
Sama da shugabannin kasashe 50 ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kungiyoyin kasa da kasa da kuma manyan yan kasuwa ne suka halarci babban taro a kan dumamar yanayi da aka yi a birnin Paris, kasar Faransa da zummar daukar matakan shawo kan wannan matsala.
Rundunar sojojin kasa ta Najeriya ta kawo karshe taronta na shekara na wannann shekarar 2017 a birnin Ibadan jihar Oyo. Taron ya tattaro kwamandodji rundunar sojin na kasar da kuma hukumomin jihar Oyo karkashin jagorancin Gwamna Abiola Ajimobi.
Domin Kari