Babban jami’aiyar Adawa ta bayyana matukar damuwarta da bullar wani bangaren jami’iyar mako biyu bayan babban taron jami’iyar. Tuni dai masu korafin suka kafa sabon ofishi a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Wani kusa a cikin Fresh PDP ya fada a wata gidan radiyo mai zaman kanta a Abuja cewar zasu kaddamar da shugabannin da sabuwar huskar PDP a cikin watan Janairu mai zuwa idan Allah ya kaimu. Fresh PDP tace abin kunya ne jami’iya kamar PDP bata kundin bayanai kana ba sunayen shugabanninta a kan na’ura mai kwakwalwa.
Shugaban kwamitin amintattun PDP Sanata Walid Jibrin ya yi kira ga wadannan mutane da su dawo su rufawa sabon shugaban baya ya tafiyar da jami’iyar. Sanata Walid yace yan sabuwar PDP sun tuntubeshi, amma yace matakin da suka dauka ya saba ka’ida.
Facebook Forum