A cikin hudubarsu ga al’umma, limaman Kristan sun gargadi mabiya addinin Krista su kasan ce jakadun Yesu Almasihu wajen wanzan da zaman lafiya musamman a wannan lokaci da ake shirin bukin ranar haifuwar Annabi Isa Alaihi Sallam. An kuma gargadi Kristoci kada su maida wannan bukin lokaci na sharholiya, amma lokaci ne da zasu nuna halaye na gari.
Shugaban darikar ECWA ta kasa da kasa, Reverend Jeremiah Gado yace Annabi Isa Alaihi Sallam ya zo duniya ne ya kawo salama ga mutane don haka wajibi ne ga mabiyansa su yi koyi da halaiyar sa. Ya kuma kabalanci yan Najeriya musamman yan Krista da Musulmi halolinsu ya nuna addinansu daga Allah ne.
Shima Pastor Daniel Manu Faruk yace ba rana ce wanda kawai za a yi shagulgula kawai ba ne, rana ce da za a tuna kaunar da ubangiji ya yiwa duniya. Yace yakamata Kristoci a wannan lokaci su karfafa ziyarar juna kuma su kara bada kyauta ga jama’a.
Facebook Forum