Bayan sa’o’i 24 kacal da samu walwalar da kuma komawa ga iyalansu, wasu da ake zaton mayakan ‘yan aware da suke fafutukar balle yakin masu amfani da harshen Ingilishi a Kamaru, sun yi kira ga shugaba Paul Biya da ya saki shugabanninsu, in dai yana son zaman lafiya a kasarsa.