An tsare Paul Whelan tsohon sojan ruwan Amurka dan asalin kasashen Birtaniya da Ireland ne a karshen watan Disemba a Moscow. Kama shi ya haifar da tsegumin cewa Rasha tana so ta yi amfani da shi domin tayi musaya da wata ‘yar kasarta da ta aikata laifin leken asiri a Amurka.
Amma mataimakin na ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya fada cewa lokacin tattaunawa a kan yiwuwar musayar Whelan da Maria Butina bai kai ba, saboda ba a riga an tabbatar da laifi a kan Whelan a hukumance ba, a cewar kamfanin dillancin labaran Rasha.
Tun da farko wasu kafafen yada labarai a Rasha sun ce wata majiya da basu bayyana ba tace akwai yiwuwar tabbatar da lafin leken asiri a kan Whelan, lamarin da ka iya kai shi gidan yari tsawon shekaru 20.
Facebook Forum