Dakarun sojin Amurka sun kai farmaki ta sama a jiya Asabar a Somalia kuma sun kashe akalla mayakan al-Shabab takwas.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Asabar cewa sakataren harkokin cikin gida Ryan Zinke da ake zarginsa da almundahana zai bar gwamnati a karshen wannan shekara.
Ma’aikatar sojin Najeriya ta dage haramcin gudanar da ayyuka da ta dorawa asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) wato UNICEF dake aiki a arewa maso gabashin kasar.
Shugaban Amurka Donal Trump ya kawo karshen cece-kuce a kan batun daukar sabon shugaban ma’aikatan ofishinsa, inda ya ambato sunan shugaban hukumar kasafin kudin kasar a matsayin shugaban ma’ikatansa mai riko wanda zai maye gurbin tsohon jami’in sojin ruwa mai ritaya John Kelly.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace yana sane da matsaya mai tsauri da ‘yan majalisun tarayyar Amurka suka dauka a kan dadaddiyar kawayensu Saudi Arabia, lamarin da ya kwatanta da abin tarihi.
Mutuwar wata yarinya mai shekaru bakwai ‘yar kasar Guatemala a hannun jami’an tsaron kan iyakar kudu maso yammacin Amurka a makon da ya gabata, ta dora ayar tambaya a kan yanda jami’an tsaron iyakar suka yiwa batun rashin lafiyar yarinyar rikon sakainar kashi.
Wata kotun kasar Canada ta bada belin‘yar Chinar nan, shugabar kamfanin sadarwa Meng Wanzhou, yayinda take jira taji ko za a mika ta ga Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar dakatar da ayyukan gwamnati idan 'yan majalisa duka ki amincewa da bada kudin gina katanga tsakanin kasar Amurka da Mexico, daya daga cikin manyan alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zabe.
Ministocin Muhalli daga kusan kasashen duniya 200 sun isa birnin Katowice na kasar Poland, domin neman hanyoyin da za a bi domin amfani da yarjejeniyar Paris ta 2015 don tunkarar sauyin yanayi.
Yawan kananan yaran da suka kamu da wata cuta mai shanye jiki yayi yawan da ba a taba gani ba a Amurka. A cewar hukumar hana yaduwar cututtuka ta CDC.
Kotu a Canada na duba yiwuwar ko zata baiwa shugabar katafaren kamfanin fasahar nan na Huawei beli, ya yin da take jiran ganin ko za a mika ta Amurka domin a tuhumeta a can.
An yi jana’izar wani hafsan sojan da ya rasu a makarantar horar da jami’an tsaro dake kauyen Tondibiya cikin wani yanayi mai cike da hazo, lamarin da ya sa danginsa da jami’an fafutuka nuna bukatar bincike don gano masababin mutuwar wannan matashi.
Daruruwan tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jihar Nejan Nigeria ne sun yi dafifi a harabar ofishin hukumar fansho ta jihar domin karbar kudadensu na sallama daga aiki da hukumar kula da kudaden fanshon ta fara biya a ranar Litinin goma ga watan Disamban 2018.
China ta baiwa jakadar Amurka a Beijing takardan sammaci a jiya Lahadi domin bayyana kalubalantar kama ‘yar China nan shugaban kamfanin fasaha a Canada da Amurka ta nemi a mika matai ta domin mata shari’a a nan Amurka a kan zarginta da damfara.
Mutumin da ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai nada sabon shugaban ma’aikacin ofishinsa, yana shirin barin babban aikinsa a fadar White House.
Hukumar asusun raya noma ta kasa da kasa ta Majalisar Dinkin Duniya IFAD a takaice ta shirya zuba jari a Zimbabwe a karon farko tun bayan shekaru da dama.
Mutanen Yamal miliyan ashirin, wato kashi biyu cikin uku na al’ummar kasar na fama da rashin abinci, sakamakon yaki da ya daidaita kasar kana ya jefata cikin talauci.
Ministan harkokin cikin gida a Faransa Christopher Castaner yace an samu kwanciyar hankali a rikicin jiya Asabar a birnin Paris duk da hargisti da aka samu nan da can, lamarin da yace bai dace ba.
Kasar Kamaru tace ta kafa wani kwamiti da zai raba daruruwar mayakan ‘yan awaren kasar da Boko Haram da makamai, wadndaa suka amince su ajiye makamansu kana a sake maida su ga jama’a.
Wata babbar jami’ar kamfanin fasaha ta bayyana gaban kotun kasar Canada a kan laifuka da Amurka ke zarginta da aikatawa mai alaka da huldan kasuwanci da kasar Iran, lamarin da ya girgiza hada-hadar kudi a duniya biyo bayan kamata.
Domin Kari