Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Sudan Na Kara Kaimi


Masu Zanga-zanga a Sudan
Masu Zanga-zanga a Sudan

Jami’an tsaron Sudan sun yi amfani da barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga a birnin Khartoum a rana na cikon goma da aka fara zanga-zanga a kan tsadar rayuwa wanda yanzu kuma ake kira ga sauyin gwamnati.

‘Yan sandan sun zubawa daruruwar masu bauta da suka fara zanga-zanga bayan sun gama sallar Juma’a a wajen babban birnin kasar barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.

Wadanda suka shedi al’amarin sun ce masu zanga-zangar sun taru a birane da dama a fadin kasar, ciki har da Omdurman da Port Sudan da Atbara da kuma Madani.

Hotonuna a kan shafukan sada zumunta sun nuna hayaki mai yana ya turnuke wasu unguwannin a cikin Khartoum inda masu zanga-zangar suka kona tayoyi.

Babbar jami’iyar adawa ta Sudanese Congress Party ta fada a jiya Juma’a cewa jami’an tsaro suna kama madugunta Omar el-Digeir, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG