Yawan mutanen da suka mutu a kasar Mozanbique sakamakon kadawar mahaukaciyar guguwar nan a makon da ya gabata da ta yi barna a wasu yankunan kudancin Afrika yah aura mutane 400 a cewar wani jami’in gwamnati, yayin da ma’aikatan ceto ke ci gaba da kokarin neman mutane.
Ana sa ran shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro da takwarar aikinsa na Amurka Donald Trump zasu tattauna a kan bunkasa huldar ciniki da ta diflomasiya a yau Talata a fadar White House.
Hukumomin a Christchurch na New Zealand sun fara bada gawarwakin mutane hamsin da aka kashe a ranar Juma’a, a wani mummunar harin bindiga da aka kai wasu masallatai biyu da wani dan rajin fifita farar fata ya kai.
Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya fada a jiya Juma’a cewa za a sake bude tattaunawar zaman lafiya a Afghanistan, yana magana a kan tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da kungiyar Taliban.
Kasar Rasha tace ba zata zuba ido ta kyale takunkuman da Amurka da Canada da kuma Kungiyara Tarrayar Turai suka kakaba mata a kan harin da ita Rashan ta kaiwa jiragen ruwan Ukraine guda uku a shekarar 2018, a cikin ayyukanta na mamayar yankin Crimea a gabashin Ukraine.
A jiya Jumu’a ne wakilan Amurka da na kungiyar Taliban ta Afghanistan suka baiwa kansu wani dan gajeren hutu daga doguwar tattaunawar babu kakkautawa.
Akwai wasu alamun dake nuna cewa watakila kasar Koriya ta Arew na dab da gwajin wani makami mai linzame ko kuma harba wani kumbu, a cewar tashar rediyon N-P-R dake nan Amurka,
Wani rukunin ‘yan majalisun dokokin Amurka da suka hada da wakilan manyan jam’iyyun siyasar kasar sun la’anci gwamnatin shugaba Donald Trump kan gaza maida wa China “martanin da ya dace dangane da danne hakkin Musulmi da take yi a kasarta.”
Rangwamin haraji da kara kudaden ta take kashewa tsaro, suna cikin matakan da China zata dauka a wannan shekara domin bunkasa tattalin arzikinta dake fama da matsaloli
Hukumomin Faransa sun ce wasu bakin haure guda hamsin da suka saci hanyar su a cikin wani jirgin ruwan Faransa a wani yunkurin shinga kasar Ingila daga birnin Dover, sun isa Calais mai tasahar jirgin ruwa a arewacin Faransa a jiya Asabar.
Kasar Canada ta amince da saurare a kan batun mika babbar jami’an kudi na katafaren kamfanin sadarwar China ta Huawei ga Amurka domin fara shari’a da aka dade ana ja-in-ja a kai, wani lamarin da ka iya addabar dangantakar Amurka da Canada.
Manyan jami’an dake tattaunawa akan batun cinikayya na Amurka sun fada a jiya Laraba cewa ba a ko kusa da cimma yarjejeniyar kasuwanci da kasar China ba.
Hukumomin zabe a Najeriya suna can suna ci gaba da tattara bayanan kuri’un da aka jefa a babban zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayyar da aka gudanar a kasar jiya Asabar.
A yau Lahadi ne masu kada kuri’a a kasar Senegal zasu yi zabe domin zabo sabon shugaban kasa.
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta INEC tace jami’iyyun siyasa zasu ci gaba da yakin neman zabe kamar yanda doka ta tanadar. Hukumar zaben ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta shirya a birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta ce an maido da zaman lafiya a garin Izzi, bayan barkewar wani rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da PDP a farkon wannan makon, wanda ya yi sanadiyar kone wasu gidaje, da asarar dukiyoyi.
Masu fashin baki da masana a fannin tsaro a Najeriya sun yi nazarin kalaman Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce duk wanda aka kama ya sace akwatin zabe ya yi a bakin ransa, kalam sun kuma ja hankalin wasu da ke ganin ba daidai ba ne shugaban ya yi wannan huruci.
Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya yi kashedi a yau Talata cewa kasar sa zata gaggauta mayar da martani ga duk wani harin soja da India zata kawo mata.
Jihohi goma sha shida a nan Amurka sun kai karar gwamnatin Trump kotu game da ayyana dokar ta baci saboda ya samu kudin da zai gina Katanga a kan iyakar kasar.
Kwamandodjin rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a Somalia ta AMISOM, sun fada a jiya Asabar cewa sun amince da kaddamar da wasu sabbin ayyuka da zasu auna mayakan al-Shabab a Somalia.
Domin Kari