Yarima mai jirar gado a Saudi Arabia Mohammed bin Salman zai fara wata ziyarar wuni biyu ta farko zuwa Pakistan a yau Lahadi, inda ake sa ran zai sanar da wani aikin zuba jari na biliyoyin daloli.
Jiragen sojojin Amurka guda uku sun kai kayan taimakon da za a baiwa Venezuela a garin Cucuta na Colombia a jiya Asabar, kari a kan dubban ton abinci da magunguna da ake jira a tsallaka da su kan iyakar kasar.
Dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasa da hukumar zabe ta kasa INEC ta yi, yanzu ya janyo fushi daga masu ruwa da tsaki da kuma sauran al'ummar kudu maso gabashin Najeriya.
Bayan ta sanar da dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki, hukumar zaben Najeriya ta INEC ta na gudanar da wani taro da masu ruwa da tsaki a babban zauren taron kasa da kasa dake Abuja, inda hukumar ta bada cikakken bayani a kan dalilan da ya sa ta dage zaben na yau Asabar.
A kalla mutane 17 sun mutu a yau Talata yayin da gobara ta tashi a cikin wani babban otal a birnin Delhi da sanyi safiya, wani sabon bala’I da ya haifar da damuwa a kan matakan tsare wuta a India.
Masu tattauanawa majalisun dokokin Amurka sun cimma babbar yarjejeniya a kan bada kudaden gudanar da ma’akatun gwamnati tarayya domin hana sake rufe su a karshen wannan mako.
Shugaban kasar Saliyo ya ayyana dokar ta bace a kasar saboda yawan yiwa mata fiyade da kuma cin zarafin jima’ai da ya dabaibaye kasar.
Sarkin kasar Thailand ya yi fatali da batun shiga takarar 'yar uwarsa babba ta zama ‘yar takarar Firai Ministan kasar.
Kasashen Birtaniya da Spain da Faransa, da Sweden da kuma Denmark sun bayyana amincersu ga shugaban ‘yan adawan Venezuela a matsayin shugaban kasa mai riko.
Shugaban mujami’ar katolika na duniya Papa Roman Francis ya kai ziyara ta farko da babu wani Papa Roman da ya taba yi a yankin kasashen Larabawa inda addinin Musulunci ya samo asali.
Gwamnatin Najeriya ta gargadi kasashen ketare akan yin katsalandan a harkokin ta. Kasar da ke yankin Afrika ta Yamma ta jaddada cewa za ta gudanar da zaben shugaban kasa na gaskiya da adalci a ranar 16 ga wata Faburairu dake tafe.
Shugaban Amurka Donald Trump yace yana ganin kasa da kashi 50 na yiwuwar ‘yan Majalisar Tarayyar kasar dake kan teburin shawarwari su cimma yarjejeniyar da za ta samar da kudin gini katanga a kudancin iyakar kasar wadda zai amince da ita.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa mutane Venezuela kuma su amince da gwamnatin wucin gadin kasar karkashin jagorancin Juan Guaido yayin da yake fafatawa da shugaba Nicholas Maduro.
Kasar Kamaru tace zata girke sojojinta a kan iyakar arewacin kasar da Najeriya da kuma iyakar yammacin kasar dake yankin masu amfani da harshen Ingilishi, biyo bayan wasu sababbin hare hare da Boko Haram suka kai a arewa da kuma yankin na ‘yan awaren kasar.
Wani sabon rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya banbanta da bayanan farko da ke cewa ‘yan gudun hijira suna shiga kasashen Turai dauke da cututuka da ake iya yadawa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana ma’aikatan gwamnatin tarayya da suke aiki ba tare da an biya su albashi ba, a wannan lokacin da aka rufe wadansu ma’aikatun gwamnati a matsayin “manyan ‘yan kishin kasa”.
Wasu mutane da ba a san ko su wanene bane sun kai hari a wani gari da a ke kira Rungumawar Jawo dake cikin karamar hukumar mulkin Illela ta jahar Sokoton tarayar Najeriya.
Sabon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu Abubakar ya soke rundunar nan dake yaki da ‘yan fashi da makami wato "Federal Special Anti-Robbery Squad" ko F-SARS a takaice.
Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyib Erdogan ya fada a jiya Lahadi cewa Turkiya ta shirya ta karbin ikon birnin Manbij na kasar Syria dake hannun Kurdawa.
Wata kungiyar ‘yan ta’adda mai alaka da al-Qaida a jiya Lahadi ta dau alhakin kai hari a kan sansanin rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya da aka kai a arewacin Mali a jiya Lahadi, harin da ya kashe sojojin zaman lafiya daga Chadi guda goma kana ya jikata wasu 25.
Domin Kari