Rediyon tace wasu hotunan da taurarin dan Adam ya dauko a sansanin gudanar da binciken kere-keren makamai na kasar dake Sanumdong, sun nuna tarin manyan motoci da kanana, da jiragen kasa da kuma injunan daukan kaya masu nauyi.
Wani jami’in bincike a Cibiyar Nazarin Harakokin Yau Da Kullum Ta Duniya dake Monterey a jihar California, Jeffrey Lewis, yace daman irin alamomin da ake gani kenan a duk lokacin da Koriya ta Arewa ke shirin kera wani sabon makami kamar rokoki.
Wannan al’amarin na faruwa ne ‘yan kwannaki kalilan bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya fadi cewa zai yi mamaki matuka idan har Koriya ta Arewa ta koma ga gwajin irin wadanan makaman na nukiliya.
Trump ya fadi haka ne jim kadan bayan ganawar sa ta biyu da shugaban Koriya ta Arewa din, Kim Jong Un kwanan baya a Vietnam.
Facebook Forum