Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gab Da Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Afghanistan


Wakilan Amurka da na Taliban
Wakilan Amurka da na Taliban

Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya fada a jiya Juma’a cewa za a sake bude tattaunawar zaman lafiya a Afghanistan, yana magana a kan tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da kungiyar Taliban.

An dai yabawa Islamabad da shirya tattaunawa kai tsaye tsakanin Washington da Taliban, lamarin da jami’an Amurka suka ce ana samun ci gaba a cikin ‘yan kwanakin nan.

An shirya sake fara tattaunawa da Taliban. Da yardar Allah mu da ‘yan uwan mu zamu kasance cikin zaman lafiya a ‘yan kwanaki masu zuwa, inji Khan yana fadawa wani babban taron jama’a na kabilar Bajaur dake arewa maso yammacin kasar a cikin wata gundumar dake kan iyakar Afghanistan.

Ba tare da wani karin bayani ba, Khan yace shirin zaman lafiyar zai tabbatar da dorewar zaman lafiya da ci gaban kasuwanci da tattalin arziki a yankin, musamman kuma zai taimakawa kasar Afghanistan da yaki ya daidaita ta koma ta tsaya kan kafarta.

Jami’an Amurka da na Tliban sun kammala zaman su na baya ne a ranar Talatar da ta gabata a Qatar, inda suke fadin cewa sun cimma matakin farko na shirya kudurin yarjejeniyar da zata kawo karshen yakin da ka kwashe shekaru 18 ana yi a Afghanistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG