A daidai lokacin da ake neman bakin zaren magance matsalolin tashe-tashen hankula da rikicin Boko Haram, yanzu cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Amurka da ake kira ‘US Institute of Peace’ ta isa Najeriya tare alkawarin taimakawa don magance matsalar.
Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar tuhumar shugaban kungiyar Shi’a na kasa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da laifin kisan kai.
Majalisar dake kula da tattalin arziki ta Najeriya ta bayar da umarnin cewa a dakatar da kiwo tsakanin kasa da kasa, domin kawar da tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a Najeriya.
An shiga makon da ake rigakafin cututtuka masu saurin hallaka kananan yara a sassan duniya, wadda aka saba gudanarwa a karshen watan Afrilun kowacce shekara.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 25 ga watan Afrilu na kowacce shekara domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da ake kira Malaria.
A kalla mutum 35 ne aka kashe wasu dayawa kuma suka bace a wani harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Tse Umenger dake karamar hukumar Guma a jihar Benue.
Noma Tushen Arziki
Ciki da Gaskiya Wuka Bata Hudashi
Kwamitin farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya mayar da hankali wajen bunkasa kiwon lafiya musamman a matakin farko don inganta rayuwar al’ummar yankin.
Tsofin Shugabannin Amurka da dama na daga cikin daruruwan masu makoki da kuma addu’ar bankwana a yau dinnan Asabar ga marigayiya Barbara, matar tsohon Shugaban Amurka George H. W Bush, wadda ta rasu ranar Talata da shekaru 92.
Amurka ta ce da China da Rasha masu yada tashin hankali a duniya ne, saboda yadda su ke kin kiyaye hakkin dan adam; haka ma Koriya Ta Arewa da Iran.
Koriya Ta Arewa ta ce ta dakatar da gwaje-gwajen makaman nukiliya, kuma ta na shirin rufe wuraren gwaje-gwajen nukilyar ma.
Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da mai da ‘yan gudun hijirar Najeriya da kasar Kamaru ke yi karfi da yaji zuwa jihar Borno mai fama da tashin hankali, ta na mai bayyana hakan da saba wa dokar kasa da kasa.
Direbobi sun rufe babbar hanyar da ta hada Adamawa da jihar Taraba sakamakon matsa musu da karbar na goro da jami'an tsaro ke yi.
Rundunar sojan Najeriya ta Operation Dole ta bayyana wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da suka mika kansu a karamar hukumar Bama a jihar Borno.
A Najeriya an kawo karshen taron manyan hafsoshin sojojin Afirka da rundunar sojan Amurka ta shirya da zummar kawo karshen matsalar tsaro a nahiyar.
Kungiyar ‘yan Shi’a mabiya Ibrahim El-Zakzaky a Najeriya ta bijirewa jami’an tsaro, inda ta sake tura mutanenta suka ci gaba da yin zanga-zanga da caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
An samu hargitsi a Majalisar Dokokin Najeriya inda wasu ‘yan daba suka shiga zauren Majalisar suka dauki sandar girma.
Domin Kari