Rahotanni daag jihar Nasarawa da ke arewa maso tsakiyar Najeriya na cewa wasu mahara sun hallaka shanu sama da 70 a wani hari da suka kai wani yankin jihar.
A Najeriya, an sake bankado wasu makudan kudade da yawansu ya kai Dalar Amurka miliyan 141, da aka boye a wani asusun bankin Keystone.
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obansanjo, ya ce, shugaba Buhari da manyan jam'iyun kasar, wato APC da PDP, sun gaza kyautata makomar Najeriya, saboda haka, kada ya yi takara a 2019 a kuma kafa sabuwar jam'iya.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ba da sanarwar cewa karancin ruwan saman da aka samu a bara, ya sa al'ummar kasar cikin wani yanayi na matsalar karancin abinci.
A karon farko, hukumomin tsaron Najeriya, sun tabbatar da kasancewar mayakan IS reshen yammacin Afirka, wato ISWA a kasar, bayan wani bincike da suka gudanar sanadiyar rikice-rikicen da ke faruwa a wasu sassan kasar.
Shin wadanne fannoni ne matakin rufe ma'aikatun gwamnatin Amurka zai shafa, kuma wadanne ne ba zai shafa ba? Ga karin bayani:
'Yan sandan Najeriya sun kubutar da wasu turawan Amurka da Canada da aka yi garkuwa da su tare da cafke biyu daga cikin masu satar mutanen da safiyar yau Asabar.
A wani yunkuri na dakile yaduwar rikicin jihar Benue da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin al'umomin da ke jihar.
Ana taruka da bukukuwan tunawa da ranar da Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, ya rasu a sassan Najeriya. Sardauna shi ne Firmiyan farko na kuma karshe a yankin arewacin Najeriya.
An ji duriyar wasu daga cikin ragowar 'yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko take garkuwa da su tun a shekarar 2014 bayan da kungiyar ta saki wani sabon bidiyo.
An yi sabuwar zanga zangar lumana a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, domin ci gaba da nuna adawa da wani sabon tsarin haraji da ke kunshe a kasafin kudin bana.
Ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin man fetir a wasu sassan Najeriya duk da cewa an shiga sabuwar shekara kuma gwamnati ta ce tana daukan matakan dakile karancinsa.
A karon farko tun bayan da jami'an tsaro suka tsare shi sama da shekaru biyu da suka gabata, shugaban 'yan uwa Musulmi na Kungiyar 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El Zakzaky ya samu damar gana wa da manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya.
A Jamhuriyar Nijar yau aka fara shari’ar wasu dakarun kasar cikinsu har da wadanda ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Isuhu Mahamadu a shekarar 2015.
Kungiyar malamai reshen jihar Kaduna, (NUT), ta yi biris da barazanar da gwamnatin jihar ta yi na cewa za ta ladabtar da duk wani Malami da ya ki koma wa bakin aikin, bayan da ta shirya shiga yajin aiki a yau Litinin.
Dakarun Najeriya sun ce sun yi nasarar kashe shugaban wani gungun da ya shahara wajen yin garkuwa da mutane wanda ake zargi da shirya kisan garin Omoku na jihar Rivers a ranar sabuwar shekara.
An kuma samun tashin hankali a jihar Benue mai fama da rikicin makiyaya da manoma, bayan da wasu mahara suka far ma karamar hukumar Logo.
A wani lamari da wasu ke gani hari ne na daukan fansa, an far ma wasu kauyuka uku a yankin karamar hukumar Lau da ke jihar Taraba, harin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Koda yake hukumomi sun musanta salwanta rayuka da dama.
Bayanai daga yankin Madagali na jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani bam da aka dasa a bakin hanya ya yi sanadin mutuwar wani yaro.
Yayin da aka shiga sabuwar shekara shugaban kasar Nijar Muhamadu Isuhu ya kudiri anniyar bude wasu sabbin barikin sojoji don karfafawa dakarun kasar gwuiwa a shekarar ta 2018.
Domin Kari