Yayin jawabinsa na murnar sabuwar shekarar 2018, Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sha alwashin cewa ba za su raga wa wadanda suka haddasa matsalar karancin man fetir a kasar ba yana mai cewa za a dauki duk matakan da suka dace domin hana sake aukuwar hakan.
A wani mataki da suka dauka na nuna rashin gamsuwarsu da kamun ludayin gwamnatin shugaba Muhammadou Isufu, gamayyar jam’iyun adawa a Jamhuriyar Nijar ta gudanar da zanga zangar lumana a Birnin Yamai.
'Yan Najeriya na ta tafka muhawara a shafin sada zumunta na Facebook tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin sunayen wadanda za su shugabanci hukumomin gwamnatinsa da zama mambobi, sunayen da suka kasance har da wadanda suka rasu.
Yayin da ake bukuwan Kirsimeti a Najeriya, mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbanjo ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan matsalar karancin man fetir da ke addabar kasar.
An kai tsohon shugaban Peru Alberto Fujimori asibiti daga gidan yari, inda yake zaman hukuncin shekaru 25.
Fadar Shugaban kasar Najeriya ta ce nan da wasu kwanaki masu zuwa za a shawo kan matsalar karancin man fetir da ta jefa al'umar kasar cikin mawuyacin hali.
Matsalar karancin man fetur na kara ta'azzara a wasu sassan Najeriya kamar yadda rahotanni ke nunawa yayin da hukumomin kasar ke zargin dillalan man da boye shi domin cin kazamar riba.
Mataimakin shugaba kasa a Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya lashe zaben jam'iya mai mulki ta ANC.
Masana na hasashen cewa akalar siyasar Afirka ta kudu na dab da sauyawa yayin da dubban wakilan jam'iyar African National Congress ANC mai mulki, ke shirin zaben sabon shugaban jam'iyar.
Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake sun kai hari a wata mujami'a da ke Pakistan, inda suka kashe akalla mutum tara.
An kammala taron koli na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammcin Afirka ECOWAS a Abuja, Najeriya, inda mambobinta suka hadu domin tattauna matsalolin yankin.
Ana ci gaba da sukar matakin da wata jami'a ta dauka na hana wata daliba shiga zauren rantsar da daliban lauyoyi da za su kama aiki, saboda ta saka hijabi hade da kayan lauya a jami'ar Ilori da ke jihar Kwara.
A yau Alhamis, Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya yi watsi da zargin cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na bara.
An samu wata fashewa a birnin New York da ke Amurka, kuma hukumomi sun ce har an cafke mutum guda da ake zargi da hanu.
An mika dawainiyar gudanar da hidindumun babbar jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ga sabbin shugabannin da aka zaba.
Ga dukkan alamu, zaben shugabannin babbar jam’iyar adawa ta PDP da aka yi a Najeriya a karshen makon nan ya bar baya da kura, yayin da wasu ‘yan takara suka ce ba su amince da sakamakon zaben ba.
Bayan fama da ya yi da doguwar jinya, Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Katagum Muhammad Kabir Umar rasuwa. Sarki Kabir ya rasu ne a gida bayan ya kwashe shekaru 37 yana mulkar masarautar.
Yau 9 ga watan Disamba, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakarwa kan muhimmancin yaki da cin hanci a duk fadin duniya.
Akwai alamu da ke nuna cewa, mai yiwuwa akai ruwa rana a babban taron da jam'iyar PDP mai adawa ke yi a Abuja, bayan da gwamnonin kudu maso kudu suka nuna alamun goyon bayan dan takarar da ya fito daga yankinsu a matsayin dan takarar shugaban jam'iyar.
Domin Kari