Masu fafutuka a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da sabuwar zanga zanga a Birnin Yamai, domin jan hankulan hukumomi su canza sabon tsarin harajin da suka saka a kasafin kudin bana.
Dumbin masu zanga zanga sun fita rike da kwalaye da aka yi rubutu daban-daban na batanci ga gwamnatin shugaba Muhamadu Isufu.
Wannan ita ce zanga zanga ta biyu cikin mako guda da masu fafutukar suka gudanar.
Daya daga cikin wakilan Muryar Amurka a Yamai, Sule Mumuni Barma, da ya zanta da wasu daga cikin masu zanga zangar ya aiko da rahoton cewa masu fafutakar sun ce sai inda karfinsu ya kare.
Kungiyoyin wadanda suka hada har da masu kare muradun yara sun yi wannan bore cikin lumana ne domin tankwasa mahukunta su canza ra’ayi akan wasu sabbin harajin da ke kunshe a kasafin na bana.
A cewarsu, matakin zai jefa al’umar kasar cikin mawuyacin halin rayuwa.
Ita dai gwamnatin ta Nijar ta sha kare kanta kan daukan wannan mataki, tana mai cewa ba nufinta ba ne ta gallazawa al’umar kasar.
Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:
Facebook Forum