Ana kidayar kuri'a bayan kammala zaben shugaban kasa a Saliyo a zagaye na biyu a kokarin da kasar ke yi domin maye gurbin shugaba Ernest Bai Koroma wanda zai kammala wa'adinsa biyu.
Ana zaben shugaban kasa a zagaye na biyu a kasar Saliyo bayan da 'yan takara 11 suka gaza samun adadin kuri'un da zai ba su nasara.
Bayan tserewar mutanen da suka zargi Sanata Dino Melaye da saya masu makamai, 'yan sanda sun ayyana Sanata Melaye a matsayin mutumin da ake nema ruwa a jallo.
Rufe wata tashar yada labarai mai zaman kanta a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar da hukumomin kasar suka yi, ya diga alamar tambaya kan makomar kafafen yada labarai masu zaman kansu a kasar.
Gamayyar Kiristocin Arewacin Najeriya sun yi kira ga hukumomin kasar da su himmatu wajen ganin an sako Leah Sharibu, daliba daya da ta rage a hannun kungiyar Boko Haram, inda rahotanni suka nuna cewa an rike ta ne saboda ita Kirista ce.
Rahotanni daga Jamus na cewa 'yan sandan kasar sun kama korarren shugaban yankin Catalonia da ke son ballewa daga Spaniya yayin da yake kokarin ficewa daga kasar.
Rahotanni daga Najeriya na cewa daliban makarantar Dapchi da kungiyar Boko Haram ta sace ta kuma sako su, sun koma gida bayan da aka kai su Abuja, babban birnin Najeriya.
Korea ta Arewa ta amince ta yi wani zama da makwabciyarta ta Kudu, domin share fagen wani taron koli na hadin gwiwa da kasashen biyu za su yi.
Ana shirin gudanar da wani tattaki a Washinton, babban birnin Amurka da wasu birane a sassan duniya, inda mahalarta za su nemi a dauki matakan tsaurara mallakar bindiga domin a kawo karshen kai hare-hare a makarantu da ke haddasa mutuwar dalibai.
A Jihar Damagaram ta Jamhuriyar Nijar, an nemi ‘yan kasuwa da su saka hannayen jari wajen gudanar da sabuwar kasuwar Dole domin su ma su amfana da ita.
Shugaban ‘Yan sandan Najeriya ya ce a Janye daukacin ‘Yan sandan da ke tsaron wasu daga cikin fitattun mutane, domin a kara samar da cikakken tsaro a kasar.
Kasa da makwanni biyu da ba da belinta, kotun da ke sauraren karar da aka shigar akan Maryam Sanda kan zargin ta kashe mijinta Bilyamimu Bello, za ta koma zama a yau, inda masu shigar da kara za su gabatar da shaidan farko.
Ana ci gaba da sharar fage domin ganin an hada shugaba Donald Trump na Amurka da takwaran aikinsa, Kim Jong Un na Korea ta Arewa domin tattaunawa kan shirin makamin nukiliyan Korea ta Arewan.
A fafatawar da ake yi tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye da na gwamnati a yankin gabashin Ghouta, kasar Turkiyya ta ce dakarantu sun yi nasarar karbe ikon tsakiyar birnin Afrin.
Michael Richard Pompeo, wanda aka fi sani da Mike Pompeo, shi ne mutumin da shugaban Amurka Donald Trump ya zaba ya maye gurbin Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson da aka kora. Karanta kadan daga cikin tarihinsa.
Sa'o'i kadan bayan da ya sallami Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, shugaba Donald Trump, ya bayyana dalilan da ya sa suka raba gari da Tillerson.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sallami Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya kuma maye gurbinsa da Mike Pompeo, shugaban Hukumar Leken Asiri Na Tsaron Kasa ta (CIA).
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kai ziyara jihar Benue domin jajintawa da kuma kiran jama’a su a zauna lafiya, saboda rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da jihar ke fama da su.
A zangonsa na karshe a ziyarar da yake yi a nahiyar Afirka, Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya isa Abuja, babban birnin Najeriya inda suka gana da shugaba Muhammadu Buhari.
Majalisar dokokin China ta amince a soke tsarin mulkin wa'adi biyu ga shugaban kasa, inda kasar za ta koma tsarin da shugaban kasa zai zauna akan mulki har zuwa iya rayuwarsa.
Domin Kari