A kasar Saliyo ana can ana kidayar kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar da aka gudanar a zagaye na biyu.
A jiya Asabar aka gudanar da zaben, yayin da ake kokarin maye gurbin shugaba Ernest Bai Koroma, wanda zai kammala wa’adinsa na biyu, na shekaru biyar-biyar
Masu kada kuri’a sun yi zabi ne tsakanin dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC, Dr. Samura Mattew Wilson Kamara, da kuma dan takarar jam’iyar ‘yan adawa ta SLPP, Julius Maada Bio, wanda ke takara a karo na biyu.
A shekarar 2012 Bio, ya sha kaye a hannun shugaba Koroma mai barin gado.
Rahotanni sun nuna cewa ba a samu tururuwar mutane zuwa rumfunan zabe ba a wannan karo, kamar yadda aka gani a zaben farko ba.
An sake zaben ne bayan da dukkanin ‘yan takara suka gaza samun kashi 55 cikin 100 na kuri’un da aka kada, adadin da ake bukata kafin a ayyana samun nasara.
Daga cikin kalubalen da wanda ya lashe zaben zai fuskanta, akwai batun farfado da kasar ta Saliyo daga mummunan bala’in cutar Ebola da ta abkawa kasar a shekarun 2014 da kuma 16.
Facebook Forum