Kungiyar Al shebab ta maida hankalinta wajen kai hare-hare a wuraren cin abinci inda sukan kashe mutane da dama. A wani hari na baya-bayan nan da ta kai a wani gidan cin abinci, kungiyar ta kashe mutane hudu.
Yayin da dubban Musulmi 'yan kabilar Rohingya ke ci gaba da ficewa daga kasar Myanmar sanadiyar hare-haren da ake zargin kai masu, Amurka ta nuna damuwarta kan yadda ake samun rahotannin cin zarafin bil adama.
Hukumomin Jihar Florida a Amurka na ci gaba da yekuwa ga al'umar yankin da su fice daga gidajensu su koma tudun mun tsira yayin da guguwar da ake wa lakabi da Irma ta doshi jihar.
Ministar harkokin kasar waje ta Indonesia, Retno Marsudi, tana ziyara a kasar Myanmar domin ganawa da jagabar al’ummar kasar Aung San Su Kyi, da kwamandan rundunar sojan kasar, da kuma babban mai baiwa shugaban kasar shawara a harkokin tsaro.
Bayan ce-ce-ku-ce da aka yi ta yi tsakanin bangaren shari'ar Kenya da gwamnatin shugaba Uhuru Kenyatta, hukumar zaben kasar ta ce a watan Oktoba mai zuwa za a sake zaben shugaban kasar da kotun koli ta soke.
Amurka ta ce shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, ya kusa kure hakurinta duk da cewa ba wai Amurkan na son tsunduma cikin yaki ba ne, kamar yadda Jakadiyar kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta fada.
Wata cuta da ake tunanin ta amai da gudawa ce, ta yi sanadin mutuwar mutane 14 a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Shugaba Donald Trump ya kwashe yinin jiya Asabar yana ziyarar mutanen da guguwar Harvey ta shafa a jihar Texas inda ya kuma yada zango a sauran sassan da guguwar ta shafa.
Gwamnatin Uhuru Kenyatta na duba yiwuwar sake fasalin fannin shari'ar kasar, bayan da kotun koli ta soke zaben da ya bashi nasara a watan da ya gabata.
Wasu kasashen duniya da masana na fargabar cewa Korea ta arewa ta sake wani gwajin makami mai linzami sa'oi kadan bayan da ta sanar da cewa ta kera babban makamin kare dangi na hydrogen bomb.
'Yan kabilar Rohingya sun musanta zargin da sojojin kasar suka yi na cewa sun kashe Musulmi masu ta da kayar baya inda suka ce su aka kai wa hari aka kashe masu dumbin mutane.
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ya amince da matsayar da kotun kolin kasar ta dauka na soke nasarar zaben shugaban kasar da ya lashe, amma kuma ya ce wannan matsaya ta tauye hakkin al'umar kasar da suka zabe shi.
A karo na biyu cikin mako guda, shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa, Melania Trump za su sake kai ziyara jihar Texas domin jajintawa mutane da kuma ganewa idununsu yadda guguwar Harvey ta yi barna a yankin.
Masu lura da al'amura na yau da kullum na cewa ga dukkan alamu, har yanzu Korea ta arewa ba ta janye da barazanar da ta ke yi na harba makamai masu linazmi ba, inda a baya-bayan nan ta harba wani da sanyin safiyar yau Talata duk da takunkumin da ake kakaba mata.
Al'umar jihar Texas da bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa, na ci gaba da samun tabbaci daga hukumomin kasar kan tallafa masu da za a yi domin su koma rayuwarsu ta da yayin da shugaba Donald Trump ya ce har ya fara magana da wasu 'yan majalisar dokokin kasar.
Rikicin manoma da makiyaya babbar matsala ce da ke yawan addabar kasashen nahiyar Afirka, lamarin da kan janyo hasarar rayuka da dumbin dukiyoyi. Hakan ya sa wata kungiya mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar d ake kira FRAPS ta shirya wani taron wayar da bangarorin biyu kan muhimmancin zaman lafiya.
Bayanai masu karo da juna sun nuna cewa hukumar samar da abinci ta WFP ta dakatar da ayyukan raba abinci a wani sansani da ke jihar Bornon Najeriya bayan da aka zargi 'yan gudun hijrar da kai wa ma’aikatanta hari saboda ana yawan basu tuwo babu sirki.
A Najeriya ana ci gaba da kiraye-kiraye kan cewa lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa gwamnatinsa kwaskwarima.
China ta fara aiwatar da matakan takunkumin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince a kakabawa Korea ta Arewa bayan da Korean ta yi gwajin makamai masu linzami.
Bayan da mahaukaciyar guguwar Harvey da ta sauka a yankin Jihar Texas a nan Amurka, yanzu mazauna wasu yankunan jihar na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa yayin da hasashe ya nuna cewa mai yiwu wa a tafka ruwan sama a yankunan.
Domin Kari