Har yanzu ana kai ruwa rana tsakanin kasashen nahiyar turai da kasashen da bakin haure ke fitowa daga nahiyar Afirka da Asiya.
Bisa kuskure, dakarun kasar Somalia sun harbe har lahira wasu fararen hula 10 a garin Bariire da ke da tazarar kilomita 55 daga Mogadishu, babban birnin kasar.
Korea ta Arewa ta yi gwajin wasu makamai masu linzami guda uku, wadanda bayanai suka nuna cewa ba su kai ga inda aka yi niyyar su kai ba.
Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun halaka mutane 15 suka kuma yi garkuwa da wasu mutane takwasa a wani kauye da ke kusa da iyakar Najeriya a yankin garin Kolofota na kasar Kamaru.
Mahaukaciyar guguwar Harvey da ta sauka a yankin Jihar Texas a Amurka ta fara shafar tattalin arzikin kasar, inda farashin man fetur da na iskar gas suka haura.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa 'yan kasar jawabi kan dabarun yadda zai tunkari yakin Afghanistan yayin da Amurkawan suka fara dasa alamar tambayar shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu kuwa?
A karon farko cikin gwamman shekaru, al'umar kasar Angola za su shiga rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da za a yi ba tare da shugaban kasar ba.
Jama'a daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga jinya ya kuma koma aiki, inda suke bayyana abinda suka fi so shugaban ya fi mayar da hankali a kai.
Kasa da mako guda bayan da wani babban kwamandan kungiyar Al Shabab ya mika wuya ga gwamnatin kasar Somalia, dakarun hadaka sun kwato wani muhimmin gari daga mayakan.
Majalisar dokokin kasar Venezuela da ‘yan adawa ke jagoranta, ta yi wani zama a jiya Asabar, inda ta yi watsi da karfin ikon da sabuwar majalisar dokokin kasar ta baiwa kanta na yin doka.
Bisa ga dukkan alamu, sakonnin Twitter da shugaban Amurka Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence suka rubuta kan tafiyar Bannon, sun nuna cewa za su yi kewar Bannon a Fadar White House, kamar yadda masu lura da al'amura ke cewa.
A na sa ran da safiyar gobe Litinin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya dawo daga jinya a London, zai yi jawabi ga ‘yan kasar, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta nuna.
A yau Asabar shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya sauka a birnin Abuja, bayan Kwashe sama da watanni uku yana jinya a birnin London dake Burtaniya.
Hukumomin kasar Spain ko kuma Andalus, sun bayyana cewa sun kashe madugun da ya jagoranci harin motar da ya kai ga mutuwar mutane sama da goma a kasar a ranar Alhamis.
Dubun wani limamin coci da ake zargi da laifin sayen yaran da aka sato ta cika bayan da ya shiga hannun 'yan sandan jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Bayan da kasar Saliyo ta yi fama da bala'in zaftarewar kasa da kwararar laka dauke da ambaliyar ruwa, lamarin da ya kai da mutuwar daruruwan mutane, hukumomin kasar sun fara jana'izar mamatan.
A Fadar White ta Amurka, an sallami babban mai bai wa shugaba Donald Trump shawara a fannin tsara dabarun tafiyar da mulki yayin da gwamnatin ta Trump ke fama da suka kan rikicin da ke da nasaba da wariya wariyar launin fata da ya faru a Charlottesville na jihar virginia.
Wasu daga cikin shugabannin kasashen yankin Latin Amurka, sun fara maida martani kan barazanar matakin soji da shugaban Amurka Donald trump ya ce zai dauka a kasar Venezuela domin dawo da tsarin mulkin dimokaradiyya.
Abokin hamayyar shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya, Raila Odinga, ya yi wani gangami tare da wasu dumbin magoya bayansa kwanaki kadan bayan da ya sha kaye a zaben shugaban da aka yi.
Wasu da ba a san ko su waye ba, sun kai hari a wajen wani cin abinci a babban birnin Burkina Faso inda mutane kusan 20 suka rasa rayukansu yayin da wasu kuma suka jikkata.
Domin Kari