Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Fara Kakabawa Korea ta Arewa Takunkumi


Shugaban Korea ta arewa, Kim Jong Un yayin wata ziyara da ya kai cibiyar da ake sarrafa sinadarai ta hanyar kimiyya
Shugaban Korea ta arewa, Kim Jong Un yayin wata ziyara da ya kai cibiyar da ake sarrafa sinadarai ta hanyar kimiyya

China ta fara aiwatar da matakan takunkumin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince a kakabawa Korea ta Arewa bayan da Korean ta yi gwajin makamai masu linzami.

Kasar China ta haramta gudanar da duk wata sabuwar huldar kasuwanci da Korea ta Arewa, kamar yadda ma’aikatar hadahadar kasuwancin kasar ta fada a wata sanarwa.

Wannan mataki da Chinan ta dauka, na daga cikin matsayar da aka cimma a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a farkon watannan.

An wallafa sanarwar ne shafinta na yanar gizon ma’aikatar, inda aka nuna cewa, wannan mataki zai fara aiki ne nan take, inda ta jaddada cewa duk wata sabuwar hulda da ta shafi mallaka ko fadada harkokin kasuwanci da wani mutum ko kamfani daga Korea ta Arewa a China, ta zama haramtacciya.

Ma’aikatar har ila yau ta bayyana cewa, ba za ta rattabu hanu akan wata sabuwar hulda kasuwanci da ‘yan China ke so su kafa ko wata masana’anta a Korea ta Arewa ba.

A farkon watannan nan ne, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da sabbin takunkumi akan Korea ta Arewa, bayan da ta yi gwajin wasu makamai masu linzami kirar ballistic, da za a iya harbawa daga wata nahiya zuwa wata, da zimmar kwance mata damarar yaki.

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG