Firai Ministan Spain ya gargadi majalisar dattawan kasar a yau Juma’a da ta dauki wani matakin doka na musamman da zai ba gwamnatin tsakiya hurumin kwace ikon ncin gashin kai na Catalonia, a wani yunkurin takawa yankin mai neman ballewa daga kasar burki.
Hukumar zaben kasar Kenya tace kimanin mutanen miliyan shida da dubu dari biyar ko kuma kashi daya cikin uku na masu rajista ne suka kada kuri’a a jiya Alhamis a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa na shekarar 2017.
Tallafin ya kai nakudi CFA milyan ashirin.
Gwamnatin jihar Sakkwato ta kaddamar da wani shirin taimakawa tsofaffi marasa galihu da basu da mataimaka da suka hada da maza da dari biyar daga sassa dabam-daban na jihar Sakkwato don saukake musu wahalhalun rayuwa da suke fama dasu.
Rundunar yan sanda jihar Ogun a Najeriya ta tabbatar da kama wasu mata da na miji da suke satar kananan yara suna sayar dasu ga masu bukata.
Da sanyi safiyar yau Asabar ne wasu yan bindiga suka kai harin ta’addanci a kan barikin sojan Ayoru dake yankin Tilaberi a Jamhuriyar Nijar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya isa Gabas ta Tsakiya a yau Jumma’a domin halartar taron tattaunawa tsakanin gwamnatin Saudiya da ta Iraqi, da kuma duba hanyoyin da za’a karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Wani sabon bincike yace abubuwa da suka fi kashe mutane kuma suke haddasa mutuwa farab daya sune yaki, ta’addanci, bala'oi daga Allah, da tabar sigari da kuma cututtuka.
Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis yace rundunar soja na binciken mutuwar sojojin Amurka hudu a Nijer da suka mutu a farkon wannan wata a hannun mayakar jihadin Islama.
Hukumar dake kula da kasuwancin kasa da kasa ta kungiyar tarayyar turai, ta haramatawa Ghana shigar da wasu amfanin gonakinta zuwa kasashen Turai a shekarar 2015. Haramcin ya shafi diyan itace da kayan lambu saboda samun wasu gurbatattun abinci da aka aike dasu Turai.
Dr. Usman Bugaje wanda jigo kuma har ya rike mukamin sakatare jam’iyyar dake mulkin Najeriya a zamanin yakin neman zabe kuma mai sharhi kan harkokin yau da kullum, ya yi tsokaci a kan batun kira da wasu yan Najeriya ke yi na sake fasalin kasar saboda gaggauta ci gaba.
Hadakar kungiyar masu fama da nakasa a jihar Taraba da suka hada da kutare da kurame da guragu da makafi da bebaye sun yi wata gagarumar zanga zanga zuwa fadar gwamnatin jihar don ta share musu hawaye
Shige da fice cikin sauki tsakanin kasashen Afrika ta Yamma na ci gaba da zama kalubale musamman ga yan kasuwa masu zirga–zirga ta kan iyakokin kasashen da suke cikin kungiyar.
Akalla yan sanda sun kashe masu zanga zanga biyu a yau Juma’a a yammacin kasar Kenya yayin da suka kai samame a kan wata tashar yan sandan da makaman gona da duwatsu a cewar yan sandan.
Shugaba Donald na shirin sanar da sabon mataki da gwamnatinsa zata dauka a yarjejeniyar shirin nukliyar Iran ta shekarar 2015 wanda Amurka da tabbatar da shi karkashin shugabancin tsohon shugaba Barack Obama.
Rundunar Kwastam ta Najeriya tareda taimakon rundunar soja ta kama buhunan shinkafa sama da dubu biyu da ake kokarin shigowa dasu Najeriya.
An gargadi matasa a kasashen Afirka ta yamma cewa su dukufa wajen neman ilimi, maimakon jefa rayukan su cikin hadari ta neman zuwa turai ala tilas.
Ministan harkokin wajen Korea ta Arewa Ri Yong Ho yace Amurka ta ayyana yaki da kasarsa kuma kasar sa zata mayar da martini, ciki har da harbo jiragen saman yakin Amurka dake yankin, idan ta ci gaba da yi mata barazana.
A yau litinin Shugaban Amurka Donald Trump yace ba abinda ya hada maganar wariyar launin fata da taken kasa da wasu manyan 'yan wasa ke bijirewa yayin da ake buga taken kasa.
An kwashe kusan mutane dubu hamsin daga dutsen Agung dake yankin Bali a saboda jami’an hukumar nazarin aukuwar bala’I ta kasar sun yi kashedin cewa akwai yiwuwar aman wuta daga dutsen.
Domin Kari