An shigar da wata kara a kotun kolin India dake kalubalantar matakin gwamnatin kasar na korar yan kabilan Rohingya da suka kai dubu dari hudu da suka arce daga Myammar.
Ana sa ran mahaukaciyar guguwar teku da aka lakawa suna Maria zata ratsa a Martinique da kuma Dominica a daren yau Litini yayin da ruwan sama ke wucewa zuwa wasu yankuna da guguwar Irma tayi barna.
Shugabannin duniya sun fara isowa birnin New York da ke Amurka, domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran batun gwajin makamin nukiliyan Korea ta Arewa shi zai mamaye batutuwan da za a tattauna a kai.
A yau Litinin ne ake sa ran mahaukaciyar guguwar nan ta Irma zata rage karfi yayin da take ratsawa zuwa arewacin Florida ko kuma Kudancin Georgia a cewar cibiyar dake nazarin muguwar guguwa ta kasar Amurka.
Shugaba Donald Trump a karon farko a matsayinsa na shugaban kasa zai jagoranci Amurkawa a yau Litinin wurin tunawa da hare haren ranar sha daya ga watan Satumban da aka kaiwa New York da Washington a shekarara 2001
Ranar 21 ga watan Agusta jihohin Amurka 50 baki daya sun sha kallon husufin rana, abinda ya baiwa daukacin al'umar Amurka damar ganin yadda wata ya shiga tsakanin duniyar dan'adam da kuma duniyar rana.
Karshenta dai 'yan sandan Spain sun harbe mutumin da ake zaton shine direban motar nan da akayi anfani da ita wajen kai harin ranar Alhamis da ya hallaka mutane a Barcelona har lahira.
Wasu sojin ruwan Amurka guda goma sun bace wasu biyar kuma suka jikkata bayan da jirgin ruwan sojin Amurka mai suna "USS John S. McCaine" yayi karo da wani jirgin jigilar kayan 'yan kasuwa a gabashin Singapore kusa da tekun Malacca.
An tabbatar da mutuwar mutane goma sha tara a wata babbar girgizar kasa da ta abkawa wani yanki mai tsaunuka cikin lungu a lardin Sichuan na kasar Chana a jiya Talata.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yace shi bai ga wata barazanar tabbas da Korea ta Arewa ke yiwa yankin Guam dake tsibirin Pacific ba, duk da ikirarin Pyongyang din cewar tana gwajin dabarunta na lullube wannan yanki na Amurka baki dayansa da wuta.
Madugun yan adawar Kenya Raila Odinga yace an yi kutse mai yawan gaske da shirya rashin gakisya a kan komputocin hukumar zabe, wanda yayi sanadiyar fitar da adadin sakamakon zaben da yace na magudi ne wanda ke nuna shi a bayan shugaba Uhuru Kenyatta da rata mai yawan gaske.
Jiya Talata, senatocin Amurka suka sabunta kiraye kirayen ga shugaba Donald Trump, da ya sanya hannu nan take kan dokar da ta kunshi sabbin takunkumin da suka kakakabawa Rasha da Iran, da kuma Koriya ta Arewa,
Babban jakadan Amurka, sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson yana aikawa Koriya ta Arewa, sakonnin cewa "Amurka ba makiyar ta ba ne.
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya yayi amfani da kafofin sada zumunta na yanar gizo inda ya bayyana "bakin cikinsa" kan kashe wani babban jami'in hukumar zabe, gabannin zaben kasar da za'a yi makon gobe.
Manyan hafohin mayakan Najeriya sun isa birnin Maiduguri a jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria biyo bayan umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo cewar manyan sojojin su koma yankin da ya sha fama da hare haren yan ta’addan Boko Haram tare da yin garkuwa da mutanen yankin.
Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a yankin Afrika ta Yamma a Argungu ta jihar Kebbi.
Hukumomin kasar jamhuriyar Nijar sun kaddamar da makon fadakar da al'ummar kasar amfanin shayar da kananan yara nonon uwa, domin rage yawan mace macen kananan yara daga sabin haihuwa zuwa yan shekaru biyar a duniya
Shugaban sojojin Nigeria Laftanan Janar Yusuf Tukur Buratai yace tilas ne sassan sojin kasar su yi aiki tare wurin cimma nasara a yaki da yan ta’addan Boko Haram da masu satar mutane da kuma kawo karshen tashe tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma
Rasha ta ce za ta kori jami'an diplomasiyar Amurka kusan 800 da ke aiki a kasar a matsayin martani kan sabbin takunkumi da Amurkan ta kakaba mata.
Kai ruwa rana da ake yi tsakanin shugaba Donald Trump na Amurka da babban lauyan gwamnatin kasar Jeff Sessions na kara ta'azzara yayin da Sessions din ya ce ba shi da niyyar yin murabus.
Domin Kari