Jami’an tabbatar da bin doka da oda na Amurka sun bada sanarwa a jiya Alhamis cewa an kama membobi kusan 300 na wata kungiyar daba mai suna MS-13, mummunar kungiyar tada fitina da gwamnatin Trump ta lashi takobin kawarwa daga titunan Amurka.
Dadadden shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya yi fitowar farko a bainar jama’a a yau Juma’a, tun bayan da sojojin kasar suka masa daurin talala a farko farkon wannan mako.
Gwamnatin Burundi tace ba zata bada hadin kai ga kotun manyan laifukan ta kasa da kasa ta ICC a kan aniyarta na gudanar da bincike a kan zargin take hakkin bil adama a kasar.
Wani binciken da hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD ta gudanar tsakanin yan gudun hijiran kabilar Rohingya da suke zaune a Bangladesh da yawansu ya haura rabin miliyon, ya nuna kashi daya cikin uku masu rauni ne kuma suna bukatar taimako na musamman.
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta gabatar da wasu mutane wa manema labarai su guda arba’in da biyu wadanda ake zargi da aikata laifuka da dama a helkwatan yan jihar a Bauchi. Ana tuhumar su ne da laifuka kamar satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makamai da sauransu.
Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun rushe kungiyar wasan kokawa ta kasar da nufin kawo karshen rikicin shugabancin da ya barke tsakanin mambobin hukumar wanda yaki ci yaki cinyewa kuma hukumomin ke kallonsa hanyar tabarbarewar wasan kokawa a Jamhuriyar Nijer.
Wata kotu a kasar Zimbabwe a jiya Asabar ta bada umarni daure wata yar asalin kasar Amurka a gidan yari yayin da ake tuhumarta da cin mutunci da nuna rashin da’a ga shugaba Robert Mugabe.
A jiya Asabar ne aka fara aikin bada rigakfi cutar kwalara ga dubban kananan yaran yan kabilar Rohingya da suke gudun hijira Cox Bazar dake kasar Bangldesh a huska ta biyu.
Jajircewa wajen neman ilimi a kowane fannin rayuwar dan Adam da kuma aiki da shi sune batutuwan da suka mamaye taron laccar da kwalejin Excel dake Kano ta shirya a jiya asabar, a wani bangare na yunkurin fadakar da Jama’a kan bukatar rungumar ilimi domin kawar da fitintunu a tsakanin al’uma.
Hadakar kungiyar masu motocin dakon kaya a jamhuriyar Nijer sun yi barazanar shiga yajin aiki muddin aka ci gaba da sabon shirin haraji akan su.
Kungiyar yan bindigar Avengers ta yankin Naija Deltan Najeriya ta lashi takobin sake koma ga kai hare hare da take kaiwa kan kamfanonin mai a yankin.
Ministan harkokin wajen Cuba ya zargin Amurka da gangan ta yi karya game da harin wata cutar da ba a gano sanadinta ba a kan jami’an diplomaisyar Amurka a Cuba
Wasu ‘yan kasar Korea ta Arewa guda hudu da suka arce daga kasar su sun shaidawa Muryar Amurka a wasu sakonni bidiyo abubuwan da suke son shugaban Amurka Donald Trump ya yi da kuma abubuwan da suke ganin yakamata ya fada a ziyarar da zai kai Korea ta Kudu.
Ana sa ran sake farfadowar tattalin arziki a Afrika ta Yamma a cikin wannan shekara tun bayan shekaru 20 da tattalin arzikin yankin ya tabarbare ya zuwa shekarar 2016, a cewar wani rahoton Asusun lamuni ta kasa da kasa ta IMF da ta saba fitarwa a kowane shekaru biyu biyu.
Sarakunar gargajiya a jihar Adamawa sun fara fadakar da al’ummarsu game da zuwa yin rajista don samun daman yin zabe a shekarar 2019. Wannan fadakarwar tana zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zabe ta INEC take kara wa’adin sabunta katin zabe.
Taron gangamin da kungiyoyin kare hakkin jama’a suka shirya a birnin Yamai domin nuna adawa kan kasafin kudin da gwamnatin kasar ta gabatarwa majalisar dokokin kasar, har wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi kone-konen tayoyi. Wasu suka hau kan tituna da sauransu.
Majalisar jihar Borno ta dakatar da zamanta har tsawon wata guda bisa zargin da ta yi cewar ana cin zarafin wakilanta a cikin wannan lokaci. Matakin da majalisar ta dauka ya biyo bayan tuhumar da wakilin mazabar Damboa Habu Daja ya yi cewar Sanata Ali Ndume ya mareshi.
Gwamnan jihar Doso a Jamhuriyar Nijer Mallam Musa Usman, ya gargadi direbobi masu izinin tuki da su kiyaye ka’idojin tuki kuma su daina garaje a kan hanya.
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya watau NDLEA a takaice ta lalata tabar wiwi da ta kama da ya kai ton goma sha hudu. Hukumar ta yi kira ga yan Najeriya da su taimakata mata a wannan yaki da take yi yan bata gari.
Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis yace babu wani abin da ya sake a shirin Amurka na bada kariya ga Korea ta Kudu game da barazanar makaman nukiliya da masu lizzami daga Korea ta Arewa.
Domin Kari