An yi kamen ne a cikin yan makwanni a wani gagarumin shirin murkushe ayyukan 'yan daba da aka bai wa suna "Operation Raging Bull." Jamai'ai sun ce a karkashin wannan shirin da huklumar Shige da Ficen baki da kuma Kwastam ta Amurka take jagoranci, an kama 'ya'yan kungiyar MS-13 su 214 a nan cikin Amurka, yayin da aka kama wasu guida 53 a kasar El Salvador, cibiya, kuma inda wannan kungiya ta samo asalinta.
Wannan shiri mai matakai biyu na murkushe kungiyar MS-13 da hanyoyin samun kudadenta a fadin duniya, an fara aiwatar da shi tyun zamanin gwamnatin tsohon shugaba Barack Obama, amma kuma an kara tsananta shi a karkashin shugaba Donald Trump.
Babban Antoni janar na Amurka Jeff Sessions ya fada cewar wannan muhimmin mataki ne da gwamnatin shugaba Trump ta dauka a kan yan daban MS-13, wacce ake samun ‘ya’yanta a cikin manya manyan laifukan kisa a fadin kasar.
Facebook Forum