Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun harbe suka kashe wani dan jaridar Ghana da ya kware a buga labaran da suka shafi abin fallasa kuma ma’aikacin kamfanin jarida na Tiger Eye PI mai suna Ahmed Hussein Suala, a unguwar Madina dake birnin Accra.
Wata kotun gwamnatin tarayya ta samu dan tsohon shugaban kasar Guinea da matarsa da laifin bautar da wata yarinya wadda bata da takardar zama Amurka, da suka dauko daga kasarsu suka tilasa mata yin aiki a gidansu na tsawon shekaru goma sha shida ba tare da biyanta ba.
Gwamnatin kasar Kamaru tace ‘yan tawaye a jamhuriyar Afrika ta tsakiya dake makwabta sun saki ‘yan kasar Kamaru guda hudu ranar Lahadi da suka yi garkuwa da su bara.
Biyo bayan rashin halartar zaman kotun da’ar ma’aikata da babban alkalin Najeriya Walter Nkanu Onneghen ya yi bisa tuhumar rashin ambata kadarar sa, lauyoyi na ci gaba da muhawara kan tanadin doka da kuma yadda ma’aikatan shari’a ke daukar lamarin.
Wasu ‘yan bindiga a kan Babura suka kai hari da yammacin ranar Lahadi a garuruwa uku da suka hada da Warwanna da Kursa da kuma Dutse, duk a gundumar Gandi ta karamar hukumar mulki ta Rabah a jihar Sokoto.
A daidai lokacin da ake haramar zabe a Najeriya,yanzu haka wata sabuwa ta kunno inda kungiyoyin addini suka fara bayyana wadanda zasu goyawa baya a cikin yan takarar shugaban kasa,batun da ya soma jawo cece-kuce inda wasu ke ganin haka bai dace ba.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya mayarwa mai baiwa shugaban Amurka shawara kan harkokin waje John Bolton martani kan bukatar sai Turkiyya ta tabbatar da cewa bazata kaiwa mayakan Kurdawa dake Arewa maso gabashin Syria hari ba, kafin Amurka ta janye sojojinta daga kasar.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce ana ci gaba da samun karuwar matsalolin jin kai da na tsaro a iyakar da ke kudancin kasar, ya na mai kiranta a matsayin matsala mai sosa zuciya.
Rundunar sojojin saman Najeriya tayi jana'izar dakarunta da suka rasu a hadarin jirgin yakin nan na Mi-35, dake rufawa dakarun bataliya ta 145 baya a Damasak dake yakar yan Boko Haram.
An sun rarrabuwar kawuna a hadakar kungiyoyin makiyaya a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya,inda a karon farko wasu kungiyoyin makiyaya suka ce sun yafewa gwamnatin jihar tare da bayyana goyon bayansu ga jam’iyar PDP a zabe mai zuwa, yayin da wasu kungiyoyin kuma ke cewa ba zata sabu ba.
Uwargidan mataimakin shugaban Najeriya, Dolakpo Osinbajo ta gargadi al’ummar Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatansu don gudanar da zabe a zabubbukan da za’a gudanar a kasar.
Gwamnatin kasar Gabon ta kwace ikon Libreville, babban birnin kasar, bayan wani yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba, a cewar jami’an a jiya litinin.
Shugaban Amurka Donald Trump yace zai yiwa kasar jawabi a yau Talata kan abin da ya kira “matsalolin jinkai da tsaron kasa” dangane da kan iyakar Amurka da kasar Mexico, kafin ya je wurin a ranar Alhamis, saboda ya gane ma idonsa irin kokarin da ake yi na hana kwararowar bakin haure cikin Amurka.
Yayin da jam'iyyu da 'yan sisaya a Najeriya ke ci gaba da yakin neman zabe domin tunkarar babban zaben kasar da za'ayi a watan gobe, Jam'iyyar hamayya ta PDP a jihohin Jigawa da Neja tace ta daura damarar dawo da gwamnati a wadanndan jihohi.
A Najeriya Ana ci Gaba da cece kuce kan wa'adin sufeto Janar na yan sandan kasar Ibrahim Kpotum Idriss. Yayin da wani sahsen ‘yan Najeriya suka gani zai iya ci gaba da aikinsa musamman a wannan lokacin siyasa, wasu kuma na gani lada ya isa.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a Abuja tare da wasu tare da wasu kusoshin jam’iyarsa ta APC mai mulkin kasar, inda shugaban kasar ya ya gargadi yan majalisar da suyi kampe a kan ‘ka’ida da manufa mai kyau ba tare da ‘batanci ko cin zarafin kowa ba.
A yammacin jiya Litinin da misalin karfe shida ne wasu da ake zaton 'yan boko haram ne suka kai hari a kan jami’an soja a kwauyen Auno dake daf da shiga garin Maiduguri.
Ana samu bayanai mabanbanta dan gane da adadin mutanen da suka rasa rayukan su, sakamakon zanga-zangar kira da shugaba Omar Al-bashir ya sauka daga mulki, gwamnati ta ce mutane 19 amma kungiyar Amnesty International ta ce adadin ya kai mutane 37.
Yanzu haka ana ta kone-kone a jihar Ceara dake arewa maso gabashin Brazil, an fara tashin hankalin ne kwana daya bayan da aka rantsar da sabon shugaban kasar Jair Bolsonaro.
Jami’an hukumar zabe a Jamhuriyar Demokaradiyar Congo sun fada a jiya Asabar cewa zasu jinkirta fitar da sakamakon zaben shugaban kasa da suka yi niyar fitarwa a yau Lahadi har izuwa sabon mako.
Domin Kari