Shugaban hukumar zaben kasar Corneille Nangaa yace bai zai yiwu a fitar da sakamakon zaben a yau Lahadi. Yace aiki na tafiya, sai dai har yanzu basu kammala harhada sakamakon ba.
Nangaa yace hukumarsa ta samu kashi 47 ciki dari na kuru’un daga runfunan zabe a fadin makekiyar kasar dake a tsakiyar Afrika, wacce take kuma fama da hanyoyi marasa kyau.
Ya kuma ce tsarin harhada sakamakon zaben irin na da, yana cikin abubuwar dake haddasa jinkirin aikin. Hukumar tayi niyar amfani da hanyar yanar gizo ta tattara sakamakon zabe daga sassan kasar. Sai dai hukumar ta dakatar da yin hakan bayan ‘yan adawa sun yi korafin cewa hakan zai bada damar tafka magudi.
Nangaa bai bada takamaiman ranar da za a kammala tattara ko fitar da sakamakon zaben ba.
Facebook Forum