Amurka ta umarci ma’aikatanta da masu aikin gaggawa ba su fice daga Iraq, yayin da ‘yan majalisar dokokin Amurka suke bayyana fargaban shiga yaki da Iran.
Shugaban Amurka Donald Trump yana shirin sanar da tsarinsa na shige da fice a yau alhamis, tsarin da zai rage bada izinin zama Amurka bisa dalilan dangantakar iyali da kuma dalilan jinkai.
Wata jami’iyar adawa a Najeriyar mai suna Hope Democratic Party ta shigar da wata kara inda ta ce tana neman Kotun Zaben Shugaban Kasa ta dakatar da rantsar da Shugaban Kasa Mohammadu Buhari, cewar ana kalubalantar nasarar da ya yi a kotu.
Masu gabatar da kara a Sudan sun tuhumi tsohon shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir da hannu a kisan masu zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.
Kasar Saudi Arabia tace tankokinta biyu sun yi mumunar lalacewa a wani harin ganganci da aka kai da safiyar shekaranjiya Lahadi a gabar tekun Hadaddiyar Daular Larabawa. Sai dai ba a bada wani karin bayani a kan lalacewar ba.
Kasar China tace zata kakaba Haraji na dala biliyan sittin a kan kayan Amurka, da ake shiga da su kasar ta.
Biyo bayan damke mata da a ka samu su na rawa tsirara a wani gidan rawa a Jabi Abuja Caramelo da hukumar kare muhallai ta Abuja ta yi, gungun mata da rakiyar kungiyoyin da ke da’awar kare hakkin matan sun ci gaba da zanga-zanga a Abuja don nuna rashin amincewa da kamen.
Gobe Laraba al’ummar Afrika ta Kudu zasu kada kuria’a a zaben da ka iya zama kalubala mafi girma da jam’iyar ANC mai mulki zata fuskanta. Yayin da jam’iyar da abokan hamayyarta suke kokarin jawo ra’ayin masu kada kuri’a da basu yanke shawara kan jam’iyar da zasu zaba ba.
‘Yan jam’iyar Democrat a majalisar dokokin Amurka sun ce zasu sake komawa bincike kan matakin da gwamnatin Trump ta da dauka bayan guguwar Maria.
A zamanta na jiya litinin, majalisar dokoki ta jihar Kano ta tafka mahawara akan wata bukata ta kirkiro masarautu guda hudu a jihar, hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da majalisar ta kwashe watanni tana aikin gudanar da sauye-sauye a kundin dokar dake kula da ayyukan majalisar sarautar ta Kano.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace Amurka ta kimtsa ta kai gudunmuwar soja domin dakile rashin kwanciyar hankali dake faruwa a Venezuela.
An gano wata mace da mummunar rauni tare da wani yaro a yau Asabar a lokain da gyaran wata gida a Sri Lanka inda jami’an tsaro suka yi musayar wuta da wani gungun ‘yan bindiga a Kalmunai dake yankin gabashin kasar. An kwantar da matar da yaron a asibiti.
Ma’aikatar tsaron Amurka tace tana niyar aika karin sojoji dari uku a kan rundunar Amurka dake aiki a kan iyakar kudancin kasar da Mexico a aikinsu da zai basu daman kusanci da bakin haure, lamarin da ya sabawa tsarin farko na dakarun da ya hanasu kusanci da bakin haure.
Yawan karuwar al’umma a Najeriya ta sama da kashi uku cikin dari a kowace shekara, yasa hukumomin kasar suna bada magungunan tsaranta iyali a kyauta tare da bada nasiha ga iyalai a Najeriya domin rage karuwar al’umma.
Pakistan a yau Lahadi tayi kashedi ga abokiyar gabanta da take ikirarin tana shirin kaddamar da hari a kanta, lamarin da yasa Pakistan ke kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukar matakan diflomasiya domin hana India jefa yankin cikin tashin hankali da rikici.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar cewa gwamnatin Trump na niyar yanke taimakon kudi da take baiwa kasashen Guatemala, Honduras and El Salvador.
A yau Lahadi ne ‘yan kasar Turkiyar suke gadanar da zabe a fadin kasar. Ana sa ran shugaban Turkiya kasar Recep Tayyip Erdogan yana huskantar matsala a wannan zaben kuma akwai yiwuwar zai rashi tasiri mayna biranen Ankara da Istanbul.
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza sun ce rundunar Isra’ila sun harbe wani dan Falasdinu mai shekaru 21 har lahira da safiyar yau Asabar a kusa da katangar kan iyaka.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa ‘yan jarida a jiya Juma’a cewa kasar Venezuela na fama da tsananin matsaloli, yayin da wasu jami’an fadar White House suka kyankyasa batun kakabawa kasar takukuman tattalin arziki.
Tana yiwuwa attoni janar Amurka William Barr ya fara fitar da takatataccen bayaninsa a yau Lahadi, a kan rahoton binciken Robert Muller da ake masa mai rikon asiri.
Domin Kari