Kusan shekaru biyu ne Robert Muller ya gudanar da bincike a kan yiwuwar katsaland da ake zargin Rasha da aikatawa a zaben shugaban kasa a shekarar 2016 da kuma sanin ko bayan Donald Trump ya dauki ragamar mulki ya yi shisshigi a cikin aikin binciken.
Barr da rukunin ma’aikatansa sun kwashe sa’o’i a jiya Asabar suna nazarin rahoton Muller da aka hannunta musu da yammacin shekaranjiya Juma’a, binciken da aka kwashe watanni 22 ana gudanarwa. Hadiman Barr sun ce yana niyari baiwa manyan ‘yan majalisa takaitaccen bayanansa na farko bayan nazari mai yawa a yau Lahadi kuma akwai yiwuwar zai fitar takaitaccen bayanin ga jama’a
Kusoshi a majalisun kasar, da suka hada da ‘yan adawan Democrats da takwarorin su na Republican na shugaba Trump, sun yi kira da a bayyanar da cikakken rahoton, amma dai akwai shakku ko Barr zai yi hakan. Trump ya fada a makon da ya gabata cewa bashi da wata damuwa idan aka fitar da cikakken rahoton ga jama’a, amma kuma yace yin haka na hannun Barr ne, wanda ya nada shi ya jagorancin sashen dokokin kasar kuma shine zai yanke shawarar abin da zai fitar ga jama’a.
Facebook Forum