Rahotanni daga yankin Makalondi dake kan iyakar jamhuriyar Niger da kasar Burkina Faso sun ce wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani mai wa’azin addinin krista dan asalin kasar Italiya a daren jiya Litinin, yayinda hukumomi ke cewa an tura jami’an tsaro domin su ceto shi.
Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan Ali, tare da Ministan tsaron Jamhuriya Nijer Kalla Moutari, Talata 18 ga watan Satumba shekara 2018 suka rattaba hannu , akan yarjeniyar Inganta tsaro akan iyakokin kasashen biyu.
A Jamhuriyar Nijar an shiga takun saka tsakanin kungiyar alkalan Shari’a da hukumomin kasar, sanadiyar zargin wasu gwamnoni da laifin kin mutunta hukuncin kotu abin da gwamnatin ta Nijar ta ce babu kamshin gaskiya a tare da shi.
A jamhuriyar Nijer kungiyar ''SAMAN, ta alkalan shari’a, ta nuna bacin rai akan yadda masu fada a ji a kasar ke kin mutunta hukuncin kotu, haka ya sa kungiyar ta bukaci shugaban kasa Mahamadou Issouhou, ya tsawata wa masu wannan muguwar dabi’a dake barazana ga dimokradiya.
Alhazan jamhuriyar Nijer sun fara nuna kosawarsu kan jiran jirgin da zai mayarda su gida bayan kammala aikin hajjin bana. Daya daga cikin wakilan tsare tasren hajjin kasar ta Nijer Alhaji Bukari Zilli ya sanar da cewa an gama komai na soma dakon alhazan daga gobe 6 ga watan Satumba zuwa Nijer.
A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifyar wani dan Majalisar Dokoki a kauyen Gueskerou dake yankin Diffa, suna neman a biya su kudin fansa.
Jama’ar jamhuriyar Nijer sun nuna juyayi akan rasuwar tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Anan wanda Allah ya yiwa cikawa a shekaranjiya asabar. Suna masu yiwa marigayin kyaukyawar shaida saboda gudunmuwar da ya baya a fannoni da dama.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya masu kula da harkar abinci a duniya wadanda suka hada da WFP da FAO da IFAD sun amince zasu tallafawa jamhuriyar Nijar da Dala Biliyan 1.2 wanda kasar ke bukata domin gudanar da ayyukan raya karkara a tsawon shekaru uku masu zuwa.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya masu kula da harkar cimaka da suka hada da WFP da FAO da IFAD sun amince zasu tallafawa jamhuriyar Nijar da Dala Biliyan 1.2 da kasar ke bukata, domin gudanar da aiyukan raya karkara a tsawon shekaru uku masu zuwa.
Hukumomin kiwon lafiyar al’ummar a Janhuriyar Nijer sun bada sanarwar mutuwar mutane 26 daga cikin mutane kusan 1500 da suka kamu da cutar amai da gudawa a gundumar Madarunfa dake yankin Maradi.
Ya yin da al’umar musulmi ke shirin gudanar da shagulgulan babbar sallah, kasuwannin dabobi a birnin Yamai na jamhuriyar na fama da rashin ciniki.
Jam'iyar Adawa na ci gaba da cece kuce akan Yarjejeniyar gyara fadar shugaban jamhuriyar Nijar da wani kamfanin Indonesia zaiyi
Jam’iyar CDS Rahama ta bada sanarwar korar wasu makarrabanta wadanda tace suna yin zagon kasa da nufin haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yayanta sai dai wadanda matakin ya shafa sun ce ba za ta sabu ba.
An kawo karshen shari’ar da aka dade ana yi tsakanin kasar Nijar da kamfanin Birtaniya dake yin Fasfo na Africard.
Hotunan gidajen da suka ruguje a wani kauye dake kewayen Yamai a Jamhuriyar Nijer sakamakon ambaliyar ruwa.
A jamhuriyar Nijar matasan kirista na Majami’ar Evangelique sun fara gudanar da taronsu na kasa karo na 45 a birnin Yamai
Masu rajin kare demokaradiya a jamhuriyar Nijar sun maida martani bayan da shugaban kasa Mahamadou Issouhou ya dora alhakin koma bayan ilimi a wuyan dalibai da malaman kasar.
A Janhuriyar Nijer kungiyoyin nakasassu sun yi zaman dirshe a yau da safe a harabar ma’aikatar ministar jin dadin al’umma da nufin nuna rashin jin dadinsu akan abinda suka kira tauye hakkokin su.
Domin Kari