Hukumar tace labarai a Nijar CSC ta maida martani bayan da kungiyoyin ‘yan jarida suka zargeta ta nuna halin ko in kula akan matakin rufe wasu kafafe masu zaman kansu da ma’aikatar haraji ta kaddamar a ‘yan kwanakin nan saboda rashin biyan haraji.
A Jamhuriyar Nijer, jarabawar ajin karshe a makarantun share fagen shiga jami’a da aka gudanar a tsakiyar watan nan na Yuli ta bar baya da kura bayan da wata cibiyar jarabawa ta bayyana sunan wani dalibin da ya rasu a jerin wadanda suka yi nasara.
Shugabannin masu fafutukar da kotun birnin Yamai ta sallama daga kurkuku a ranar Talatar da ta gabata, sun sake jaddada anniyar ci gaba da gwagwarmaya har sai sun sauyawa hukumomin kasar ra’ayi a game da dokar harajin 2018 saboda a cewarsu talakawa na dandana kuda a sanadiyyarta.
Kotun birnin Nyamai ta umurci hukumomin jamhuriyar nijer su sallami jami’an fafitikar da suka garkame a gidajen yarin yankin Tilabery tun a ranar 25 ga watan Maris saboda zarginsu da gudanar da zanga zanga ba da izinin hukuma ba
A karshen ziyarar tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa akwai bukatar cikin hanzari majalisar ta canza ra’ayi daga dari darin da take da shi wajen bada kudaden gudanar da rundunar hadin guiwar G5 Sahel domin murkushe kungiyoyin ta’addancin da suka addabi yankin Sahel.
Mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta fara ziyara a Jamhuriyar Nijar, domin tattauna hanyoyin magance matsalolin mata a fannoni da dama kamar batun auren wuri da rashin baiwa mata dama a harkokin siyasa.
A Jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar da hadin gwiwar kamfanin Soumma na Turkiyya sun kaddamar da ayyukan gyare-gyaren filin jirgin saman Diori Hamani da ke Yamai a ci gaba da shirye-shiryen taron shugabannin kasashen Afirka da Nijar din za ta karbi bakuncinsa a 2019.
Yayinda Amurkawa ke bukin tunawa da ranar samun ‘yancin kan kasar, ofishin jakadancin Amurka a Nijar ya shirya liyafar cin abinci domin karrama wannan rana ta 4 ga watan yuli.
Wata kotun birnin Yamai ta dage shara’ar da ya kamata a yiwa wasu jami’an fafitika a jiya talata ba tare da bayyana dalilanta na daukar wannan mataki ba lamarin da ya fara haddasa shakku a wurin lauyoyin dake karesu.
A Jamhuriyar Nijar, rikicin cikin gida ya ɓarke a jam’iyyar CPR Inganci bayan da shugabanta na ƙasa baki daya Kasim Moukhtar ya rushe kwamitin gudanarwar jam’iyyar a reshenta na Yamai yayin da waɗanda matakin ya shafa suka ce ba za ta saɓu ba.
Karancin sinadarin Iodine a jikin dan adam wani abu ne da masana suka gano cewa yana haifar da matsaloli da dama wa lafiyar dan adam.
Kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar ta umurci majalisar dokoki ta dauki matakan maye gurbin jagoran ‘yan adawa Hama Amadou a majalisar wanda kotun daukaka kara ta birnin Yamai ta yankewa hukunci zaman gidan kaso na tsawon shekara 1 saboda samunsa da laifi a wata badakalar da ta shafi safarar jarirai.
Yayinda a yau 12 ga watan Yuni kasashen duniya ke bukin tunawa da ranar yaki da bautar da yara kungiyoyin kare hakkin yara kanana a jamhuriyar NIJER sun shawarci gwamnatin kasar ta kara jan damara domin tunkarar wannan matsala dake neman turjewa matakan da aka dauka a can baya da nufin takawa wannan mumunar dabi’a burki.
Jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki a Jamhuriyar Nijer ta maida martani bayan da wasu daga cikin kawayenta suka bada sanarwar kafa wani sabon gungu da zummar kalubalantar gwamnatin kasar yayin da bangaren ‘yan adawa ke murna da kafuwar wannan kawance da suke ganin zai karfafa masu gwiwa.
Rahotanni daga garin Diffa na cewa a wajejn karfe goma na daren jiya litinin wasu 'yan kunar bakin wake suka kutsa wata makarantar allo dake unguwar Diffa Kura inda suka tayar da bama bamai.
Hukumar zabe a jamhuriyar Nijar ta fitar da jadawalin zabubbukan da za a gudanar a kasar domin ba ‘yan siyasa damar fara daura damara tun da wuri, abinda jam’iyya mai mulki ke cewa ya yi daidai a yayin da ‘yan adawa kuwa ke ci gaba da kauracewa ayyukan wannan hukuma da suke yiwa kallon ‘yar amshin shatan gwamnati.
‘Yan Najeriya mazauna Jamhuriyar Nijar sun gudanar da zaben mutanen da za su jagoranci kungiyarsu a ci gaba da kara inganta matakan samar da hadin kai tsakanin ‘yan kasar a duk inda suke.
Domin Kari