Yayin da Jam’iyyar adawa ta CDS RAHAMA ke shagulugulan cika shekaru 27 da kafuwarta shuwagabanin jam’iyar sun kudiri aniyar mayar da ita a matsayinta na fil azal.
Hukumar ‘yan sandan da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta cafke wasu mutane lokacin da suke kokarin shiga kasar jamhuriyyar Niger da wasu dinbin kwayoyi.
Yanzu haka likitocin da su ke aiki a karkara a Janhuriyar Nijar sun koka akan mawuyacin halin da suke ciki na rashin biyan su albashi, da kuma rashin kayan aiki, inda su ka ce za su fara yajin aiki a cikin wannan wata na Disemba.
An yi jana’izar wani hafsan sojan da ya rasu a makarantar horar da jami’an tsaro dake kauyen Tondibiya cikin wani yanayi mai cike da hazo, lamarin da ya sa danginsa da jami’an fafutuka nuna bukatar bincike don gano masababin mutuwar wannan matashi.
An cika shekaru 70 da kasashen duniya suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar kasa da kasa ta mutunta ‘yancin dan Adam. Sai dai hukumar kare hakkin dan Adam a Jamhuriyar Nijar na ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Yan majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar sun amince da kasafin kudin shekara mai zuwa, wato 2019, amma 'yan adawar kasar da kungiyoyin kare hakkin fararar hula sun sa kafa sun shure kasafin kudin saboda wasu kurakurai dake cikinsa.
Hukumar ‘yan sandan jamhuriyar Nijar, ta yi nasarar cafke wasu ‘yan fashin da makami cikinsu har da wadanda suka hallaka wani direban tasi lokacin da suke kokarin kwace masa mota a wata anguwa a birnin Yamai.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar kafa dokar ta baci a wasu gundumomin yankin Tilabery, da nufin baiwa jami’an tsaro cikakken hurumi a yakin da kasar ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda da na ‘yan fashin da suka addabi jama’a.
Al’umomi a Jamhuriyar Nijar suna kira ga hukumomi su dauki matakin magance matsalolin Boko Haram da suke kara zafafa kai hare hare da aikata wasu miyagun ayyuka a ‘yan kawanakin nan a yankin Diffa inda satar mata da yara kanana domin neman kudin fansa ke kokarin samun gindin zama.
yanzu haka wasu yan bindiga sunyi awon gaba da wawsu 'yan mata goma sha biyar a cikin garin Tamur dake Jihar Diffa, lamarin da ya tada wa mutane hankali sosai. 'yan majalisun yankin sun yi kira da gwamnati ta tashi tsaye sosai akan harkokin tsaro.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana janye wani shirin karbar bashin biliyan 1 na dalar Amurka daga EXIMBANK na kasar China sakamakon abinda ta kira rashin mutunta alkawalin da bangarorin biyu suka dauka a yarjejeniyar da suka sakawa hannu a shekarar 2013.
A jamhuriyar Nijar jam’iyun adawa sun gudanar da jerin gwano hade da gangami a birnin Yamai da nufin kalubalantar gwamanatin PNDS TARAYYA da suke zargi da rashin iya mulki lamarin da suke yiwa kallon wata babbar barazana ga dimokaradiyar kasar.
A cigaba da yinkurinta na kare Janhuriyar Nijar daga illar 'yan ta'adda, Rundunar Sojin Janhuriyar ta Nijar ta kakkabe 'yan ta'addan da a baya su ke tayar da kayar baya a yankin kan iyakar Tilabery
A Jamhuriyar Nijer 'yan adawa Sun fice daga zauren taron kwamitin da aka dorawa alhakin kwaskware kundin zaben kasar bayan da aka samu rarrabuwar kawuna akan wasu mahimman dokokin da ke kunshe a wannan kundi da 'yan hamayya ke yiwa kallon haramtacce.
Shugabanin Kungiyar G5 Sahel da na hadin guiwar kungiyoyin Alliance SAHEL sun gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar a ci gaba da neman hanyoyin inganta rayuwar jama’ar yankunan da matsalar tsaro ta jefa cikin halin zaman dar- dar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 17 ga watan Oktoba domin bukin tunawa da ranar yaki da talauci, wace ta samo asali a 1992 bayan da aka gano cewa talauci na kokarin samun gindin zama a kasashe masu tasowa.
Wata kungiya mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar ta yi kira ga Gwamnati game da muhimmancin baiwa ‘yan mata damar morar ‘yancin da dokokin cikin gida dana kasa da kasa suka yi tanadi domin su.
Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijar ya shirya wani bukin musamman domin karrama Dr Paul Sereno wani dan kasar Amurka dake karantarwa a jami’ar Chicago sakamakon nasarar da aka samu a yayin wani aikin binciken da ya gudanar a gidan ajiyar kayayakin tarihi
Domin Kari