Harakoki sun fara dawowa sannu a hankali a jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar inda jama'ar yankin ta fara komawa kan ayyukan yau da kullum bayan da aka fara shawo kan matsalar tsaron da aka yi fama da ita a shekarun baya.
Yau talata hukumomin jihar Diffa, Jamhuriyar Nijar, suka jagoranci ayyukan kwashe wasu daruruwan ‘yan gudun hijira zuwa garinsu na asali a ci gaba da daukan matakan farfado da tattalin arzikin jihar bayan shafe shekaru kusan 6 tana fama da hare haren kungiyar Boko Haram.
Kotun ECOWAS ta umurci hukumomin jamhuriyar Nijer su biya diyyar million 50 na cfa domin shafe hawayen wani dan gwagwarmayar kasar da ya shafe watanni 18 a kurkuku bayan da ya kira wani gangamin nuna adawa da dokar harajin kasar a shekarar 2018.
A Jamhuriyar Nijar wata kungiyar kare hakkin jama’a ta bude layin waya da nufin tattara koke-koken jama’a masu nasaba da toye hakkin dan adam.
A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan kasar sun fara maida martani bayan kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a gidan kakakin majalisar dokokin kasar Seyni Oumarou dake birnin Yamai a ranar Asabar 12 ga watan Yuni.
Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta nada tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou da shugaban Nana Akufo Addo na Ghana a matsayin gwarazan tattara kudaden yaki da ta’addanci.
Da yake mayar da martani ga masu korafi akan wannan aiki dan majalisar dokokin kasa Hon. Lawali Ibrahim Mai Jirgi na cewa, bai ga laifi bai idan aka saka ‘yan majalisa cikin kyakkyawan yanayin aiki.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bada sanarwar sake bude iyakokin kasar da nufin baiwa jama’a damar zirga-zirga a tsakanin kasar da kasashe makwafta amma da sharadin nuna takardar shaidar gwajin cutar COVID-19.
Kungiyar Amnesty International ta bukaci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin baiwa dan gwagwamaryar nan Anas Djibrilla damar ganawa da lauyansa bayan da ya shafe watanni kusan 3 a garkame a gidan kason Koutoukale saboda zarginsa da yunkurin kifar da gwamnati.
kungiyar ROTAB mai fafutukar ganin an yi haske a sha’anin ma’adanan karkashin kasa ta bukaci gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauki matakan da za su bada damar rajistar mutanen da ayyukan shimfida bututun man Nijar-Benin zai raba da gonakinsu don ganin ba a manta da kowa ba wajen biyan diyya.
A yayin da ake shirin bikin tunawa da zagayowar ranar yaran Afrika ta 16 ga watan Yuni wata kungiyar kula da kare hakkin yara kanana CONAFE Niger da kungiyar MDM ta kasar Belgium, sun shirya wani taro domin horar da likitoci dubarun baiwa yara kariya daga annobar covid 19.
Yau talata 15 ga watan Yuni ake fara zagaye na 2 na kamfen riga kafin cutar covid 19 a jamhuriyar Nijer inda za a kafa asibitocin tafi da gidanka a mashigar ma’aikatun gwamnati tashoshin shiga motocin haya da filayen jirgin sama da gidajen hakimai da masu unguwa .
Hukumomin kiwon lafiyar al’uma a Jamhuriyar Nijar sun shirya wani babban gangami da nufin karrama ranar masu bada jini ta duniya wacce ake shagulgulanta a ranar 14 ga watan Yuni a ko ina a duniya da nufin ganar da jama’a mahimmancin bada gudunmowar jini a asibitoci.
Wannan shi ne karo na biyu da ake kai hari a gidan shugaban jam’iyar MNSD Seini Oumarou a kasa da shekara daya.
‘Yan Nijar kamar sauran takwarorinsu na kasashen Afrika renon Faransa sun fara maida martani bayan da shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana shirin janye sojan kasar daga yankin Sahel.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi OCRTIS a Jamhuriyar Nijar ta shigar da kara a kotu bayan da wata jarida mai zaman kanta dake da ofishi a kasar Switzerland ta ruwaito wani labari dake cewa wani bangare na tabar wi-wi da aka kama a Nijar a watan Maris din da ya gabata ya koma wajen mai shi.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya gana da shugabanin kungiyoyin fararen hula a fadarsa inda suka tantauna kan,wasu mahimman batutuwan da suka shafi tafiyar kasa a ci gaba da neman hanyoyin magance matsalolin da aka yi fama da su a baya.
Faransa ta fada a ranar Alhamis cewa za ta dakatar da ayyukan soji na hadin gwiwa tare da sojojin Mali bayan juyin mulkin da kasar ta yammacin Afirka ta yi a karo na biyu cikin wata tara.
Tawagar jami’an hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Burkina Faso, ta kai ziyara Nijar da nufin karawa juna sani sakamakon abinda aka kira jajircewar hukumar kare hakkin dan adam ta Nijar wato CNDH wajen fito da sahihan bayanan cin zarafi da toye hakkin jama’ar kasar ba tare da nuna son rai.
A Jamhuriyar Nijar, ‘yan kasar sun yaba da nasarorin da sojojin kasar suka fara samu da hadin gwiwar takwarorinsu na rundunar MNJTF a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’adda.
Domin Kari