A Jamhuriyar Nijar hukumomin kiwon lafiya da hadin gwiiwar kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da karfafa matakai domin riga-kafin cutar yoyon fitsari yayin da a wani bangare aka fara yunkurin kawo karshen kyamar da mata masu fama da wannan cuta ke fuskanta a sahun al’uma.
Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta yi na’am da manufofin siyasar da gwamnatin kasar ke fatan zartarwa a tsawon shekaru 5 na wa’adin mulkin shugaba Mohamed Bazoum.
Duk da matakan da gwamnatin Nijar ta dauka a shekarun baya-bayan nan don ganin kasar ta samu ci gaba a alkaluman kididigar da hukumar UNDP ke fitarwa a kowace shekara kan batun ci gaban rayuwar jama’a, da alama har yanzu tsugune bai kare ba.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yi karin haske game da abubuwan da suka faru da wasu ‘yan kasar mazauna Cote d’Ivoire sakamakon yamitsin da ya barke ranar Larabar da ta gabata a birnin Abidjan inda aka kwashi ganima a shagunan ‘yan Nijar, aka yi masu duka kafin hukumomin Cote d’Ivoire su dauki mataki.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya kaddamar da farautar mahandama dukiyar jama’a a karkashin shirin da ake kira Operation ‘’Ba-sani Ba-sabo’’ inda tuni bincike ya rutsa da wani babban jami’i a fadar shugaban kasa saboda zarginsa da handame miliyoyin cfa.
Kungiyar tsofaffin Ministoci da manyan jami’an diflomasiya na Jamhuriyar Nijar ta yi kira ga hukumomi da su farka daga barci don tunkarar matsalar tsaro dake kara tsananta a jihar Tilabery, inda yanzu haka dubban mazauna garuruwan da ke kusa da iyakar Mali suka fara tserewa daga matsugunnansu.
A jamhuriyar Nijer mazaunan karkarar Anzourou iyakar kasar da kasashen Mali da Burkina Faso sun fara tserewa zuwa Tilabery babban birnin jiha da nufin samun mafaka sanadiyar karuwar hare haren ‘yan bindiga a ‘yan makwanin nan, inda gwamman fararen hula da jami’an tsaro suka rasu.
A Jamhuriyar Nijar, wani ce-ce-ku-ce ya barke a tsakanin bangarorin kasar bayan da ‘yan adawa suka zargi tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou da siyen wani fili mallakar gwamnati alhali doka ba ta yarda da haka ba. Sai dai makusantansa na kallon abin tamkar rashin sanin abin fada ne.
Kwana 1 bayan da rundunar mayakan Chadi ta bada sanarwar murkushe dukkan wani kutsen ‘yan tawayen FACT, Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar General Mahamat Idriss Deby, ya kai ziyara a Jamhuriiyar Nijar a ranar Litinin 10 ga watan Mayu inda suka tattauna da shugaban kasa Mohamed Bazoum a fadarsa.
Wadansu mazauna birnin Yamai sun koka game da abinda suka kira barazanar da suke fuskanta daga wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai karfin Megawatt sama da 80 da aka kafa a tsakar gari ba tare da la’akari da ka’idodin da doka ta shimfida ba.
Yayin da ake gab da kammala azumin Ramadana, kungiyar hada kan kabilun Jamhuriyar Nijar NSC, ta shirya wani taron addu’oin zaman lafiya a wannan lokaci da kasar da makwabtanta ke fama da hare-haren ta’addanci.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rigths Watch ta bukaci gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum ta gudanar da bincike domin tantance abubuwan da suka yi sanadin mutuwar wasu daruruwan fararen hular da aka sanar cewa ‘yan ta’adda ne suka halaka su a arewacin jihohin Tahoua da Tilabery.
Shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed, ya gana da sabon kwamandan rundunar Barkhane mai sansani a yankin Sahel inda suka tattauna akan batutuwan da suka shafi yanayin tsaron da ake ciki a kasashen yankin Sahel.
An kaddamar da aikin allurar rigakafin cutar coronavirus a Jamhuriyar Nijar a ranar Talata, allurorin da kamfanonin Astrazeneca da Sinopharm suka samar.
Ranar ‘yancin aikin ‘yan jarida wani lokaci ne na bitar yanayin da ayyukan watsa labarai suka gudana a tsawon watanni 12 da suka shige.
A wani taron da ya hada masu ruwa da tsaki a fannin ilimi shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya gabatar da manufofinsa a fannin ilimi da nufin tattara shawarwarin da za su taimaka a magance tarin matsalolin sha’anin karatu a kasar na shekara da shekaru.
A Jamhuriyar Nijar, hafsan sojan da aka bayyana a matsayin wanda ake zargin ya jagoranci juyin mulki a watan Maris hade da wasu mukarrabansa sun fada hannun hukumomin kasar ta hanyar jami’an tsaron Jamhuriyar Benin
Al’umomin kasar Chadi sun fara nuna damuwa a game da yadda hukumomin suka kasa bayyana matsayinsu game da bukatar mika ‘yan tawayen kungiyar Fact ga gwamnatin rikon kwarya, wadda ta fara zargin jamhuriyar Nijar da nuna bangaranci a rikicin da ake yi.
Gwamnatin rikon kwarya a kasar Chadi ta yi watsi da dukkan wani tayin sulhu da ‘yan tawayen kungiyar FACT wadanda suka yi ikirarin halaka shugaba Idriss Deby a farkon makon jiya.
Yayin da aka yi jana’izar shugaba Idriss Deby Itno a ranar Juma'a, masu rajin kare dimokaradiya a Jamhuriyar Nijar sun gargadi ‘yan siyasa da jami’an kungiyoyin fararen hula da sojojin kasar Chadi su hada kansu don kaucewa barkewar rikici.
Domin Kari