A Jamhuriyar Nijar 'yan sanda sun kama wasu gomnan dalibai a birnin Yamai saboda zarginsu da yunkurin sata a jarabawar BAC ta ajin karshen kammala makarantun share shiga jami'a da aka gudanar a makon jiya a fadin kasar.
A ci gaba da rangadin wasu kasashen Afirka da mataimakiyar Sakataren gwamnatin Amurka mai kula da sha’anin siyasa Ambasada Victoria Nuland ke yi, jami'ar ta yada zango a Jamhuriyar Nijar inda suka gana da shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa a yammacin a ganar Alhamis.
Ranar 3 ga watan Agusta Jamhuriyar Nijar ke ta shekara 61 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallakar kasar Faransa.
Ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar mutuwar sojojin kasar kimanin 15 sannan wasu 6 suka yi batan dabo yayin da 7 suka ji rauni.
A yayin rangadin da ya fara a rasar Lahadi a jihar Maradi, shugban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bayyana shirin kara girke jami’an tsaro da karin kayan aiki a ci gaba da neman hanyoyin murkushe ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi al’umar yankin dake samun dubban ‘yan gudun hijira daga Najeriya.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun kama wasu mutanen da ake zargi da fitar da dubban miliyoyin cfa daga asusun bital malin kasar ta barauniyar hanya lamarin da wasu ke ganin za ta yiwu allura ta tono galma idan aka zurfafa binciken.
A Jamhuriyar Nijer yau ake bukin raya ranar dimokradiya wace ta samo asali daga babban taron mahawarar kasa na ranar 29 ga watan yulin 1991 wanda ya kawo karshen mulkin soja na tsawon shekaru 16.
A Jamhuriyar Nijar jam’iyun hamayya sun gudanar da taron gangami da nufin jaddadawa ‘yan kasar cewa suna nan kan bakansu na masu adawa da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum wace suke yiwa kallon mara halarci.
A ci gaba da zagayen al’umomin yankunan dake fama da matsalar tsaro Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum zai ziyarci jihar Maradi a ranakun 1 da 2 ga watan Agusta, wata guda kenan bayan rangadin da ya gudanar a jihar Diffa yankin da dubban ‘yan gudun hijira suka fara komawa garuruwansu na asali.
A Jamhuriyar Nijar ‘yan bindiga sun hallaka mutum sama da 10 a yammacin ranar Lahadi a gundumar Bani-Bangou ta jihar Tilabery lamarin da ake kallonsa matsayin wani salon hanawa manoma gudanar da aiki a wannan lokaci na saukar damana.
A Jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun fitar da sakamakon jarabawar da suka shirya a watan Nuwamban 2020 domin tantance malaman da suka cacancin aikin karantarwa a makarantun sakandare a ci gaba da daukan matakan farfado da sha’anin ilimi.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun karbi wani ruunin tallafin allurar riga kafin covid 19 samfarin Johnson & Johnson a matsayin wata gudunmowa daga gwamnatin Amurka a karkashin shirin Covax mai amar da riga kafin wannan anoba ga kasashe masu karamin karfi.
An gudanar da taro da nufin kara hada kan mata da ‘yan matan kasar Nijar a ci gaba da karfafa matakan kare hakkin mata musamman a fannin siyasa.
Majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta fara gudanar da taron gaugawa bayan da gwamnatin kasar ta bukaci a aiwatar da gyaran fuskar kasafin kudaden 2021 sakamakon sauye sauyen da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum ta zo da su.
Dakarun tsaron jamhuriyar Nijer sun hallaka gwamman ‘yan ta’adda a yammacin jiya lahadi lokacin da suka kai hari a kauyen Tchomabangou dake jihar Tilabery koda yake sojoji 4 da fararen hula 5 sun rasu a yayin wannan arangama.
A Jamhuriyar Nijar bangarorin siyasar kasar sun bayyana matsayinsu game da kamun ludayin shugaba Mohamed Bazoum wanda ke cika kwana 100 akan kujerar mulki bayan lashe zagaye na 2 na zaben 21 ga watan Fabrairun 2021.
A Jamhuriyar Nijar masu sarrafa kayan noma da kiyo sun fara gudanar da taro domin tsayar da shawarwarin da za su gabatar a taron hukumar cimaka na birnin Roma da taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a kowane watan Satumba a birnin New York.
A karshen zamanta na shekara shekara majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta shwaraci gwamnatin kasar ta kara jan damara domin kawo karshen aika-aikar ‘yan bindiga da ‘yan ta’addanda suka addabi jama’a.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da gwamnan jihar Borno Farafesa Babagana Umara Zulum sun isa garin Diffa a da hantsin ranar Alhamis inda za su tattauna akan makomar ‘yan gudun hijira.
Ranar daya ga watan Yuli shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ke soma ziyarar aiki a jihar Diffa inda gwamnatin kasar ta kaddamar da ayyukan mayar da ‘yan gudun hijirar cikin gida sama da 200,000 zuwa garuruwansu na asali a ci gaba da karfafa matakan farfado da tattalin arzikin jihar.
Domin Kari