A ci gaba da ziyarar aikin da ya fara a jamhuriyar Nijar, shugaban sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha ya jagoranci wata mahawarar bainar jama’a a birnin Yamai.
A jamhuriyar Nijer shugabanin kungiyoyin kwadago da na kungiyoyin fararen hula sun fara gudanar da taro domin nazarin hanyoyin magance matsalolin dake damun matafiya akan hanyoyin zirga zirgar kasashen Afrika ta yamma.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya yi rangadi a karshen mako a gundumar Banibangou don jajantawa al’umma rasuwar wasu mutane kimanin 69 cikinsu har da magajin gari wadanda ‘yan ta’adda suka yi wa kwanton bauna a farkon mako.
Wani harin da aka kai a karkarar Anzourou ta jihar Tilaberry a cikin dare, alhamis wayewar jiya juma’a ya yi sanadin mutuwa sojojin Nijer da dama.
Gwamnatin jahuriyar Nijer ta ayyana zaman makokin kwanaki 2 daga yau juma’a 5 ga watan Nuwamba biyo bayan mutuwar mutane kimanin 69 a gundumar Banibangou ta jihar Tilabery cikinsu har da magajin gari bayan da ‘yan ta’adda suka yi masu kwanton bauna.
Wadansu gwamman ‘yan sa kai don samar da tsaro a gundumar Banibangou ta jihar Tilabery a jamhuriyar Nijer, cikinsu har da magajin gari sun yi batan dabo bayan da ‘yan bindiga suka yi masu kwanton bauna a yayinda suke sintiri a kewayen gari.
A yayinda ake wuni na 2 na taron sauyin yanayi a birnin Glasgow na kasar Birtaniyya wasu kwararu daga jami’oin kasashen Sahel sun fara gudanar da taro a jamhuriyar Nijer.
Wata kotun birnin Yamai ta sallami Ali Tera, wani fitaccen mai hamayya da gwamnatin shugaba Issouhou Mahamadou, dan Nijer mazaunin kasar Amurka da hukumomin Nijer suka yi nasarar tuso keyarsa a shekarar 2019 suka kuma garkame shi a gidan yari.
A shekarun baya birnin Yamai na daga cikin manyan biranen da ake sakawa a jerin wadanda ke da cikakken tsaro a yankin Afrika ta yamma.
Kungiyar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta sanar cewa dubban mazaunan yankin Tilabery na cikin yanayin yiyuwar fuskantar barazanar karancin abinci sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro, inda ‘yan ta’adda suka hana gudanar da aiyukan noma a damunar da ta gabata.
Shekaru 4 bayan faruwar wannan al’mari gwamnatocin kasashen 2 na ci gaba da jinjinawa wadanan gwarazan dakaru.
Rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ta sanar da samun nasarar kama wasu ‘yan ta’adda sama da 10 a yankin iyakokin kasashen Nijer, Burkina, Faso da Mali bayan da ta bi diddigin wasu bayanan da ta samu daga al’ummar kauyukan jihar Tilabery.
Ragar 21 ga watan Satumba ake bukukuwan karrama ranar Zaman Lafiya ta Duniya da hukumar wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Nijer ta shirya wani taron tunatar da jama’a mahimmancin zaman lafiya.
Yau 1 ga watan satumba al’umar jihar Tilabery ta fara amfani da babura bayan dage dokar haramcin da hukumomin jamhuriyar Nijer suka kafa a shekarar 2018 a matsayin wani bangare na dokar ta bacin da aka kafa da nufin warware matsalar tsaron da ake fama da ita.
A jamhuriyar Nijar, kungiyoyin fafitikar kare muhalli sun gudanar da wani taron hadin gwiwa da jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin kasa da kasa.
Dakarun tsaron jamhuriyar Nijer sun yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda a kalla 100 a yayin wata rawar dajin da suka yi a kewayen kauyen Boni dake iyakar Nijer da Burkina Faso lamarin da ke kara karfin gwiwa ga al’uma a wannan lokaci da ‘yan bindiga suka hurawa fararen hula wuta.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun ayyana zaman makoki na kwanaki 2 daga yau laraba sakamakon kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa fararen hula kimanin 37 a kauyen Darey Dey na gundumar Banibangou jihar Tilabery a ranar litinin da ta gabata.
Wasu jami’an tsaron Nijar biyu sun hadu da ajalinsu a wani dajin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina lokacin da suke kokarin damke wasu ‘yan bindigar da suka sace shanu a kauyen Amore na karamar hukumar Dan Issa ta jihar Maradi.
‘Yan ta’adda na ci gaba da karkashe fararen hula a yankin Tilabery na jamhuriyar Nijer inda ko a jiya litinin ma wasu gwamman fararen hula akasarinsu mata da yara kanana suka gamu da ajalinsu sakamakon harin da ya rutsa da su a kauyen Darey Dey na gundumar Banibangou.
Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a jiya talata dadare a birnin Yamai ya hadddasa mutuwar mutane da dama.
Domin Kari