A yayin da a ranar biyu ga watan Afrilu ya cika shekara daya da dare karagar mulki, shugaban kasar Nijer ya bayyana samun nasarori a fannin tsaro a yankunan da ke fama da aiyukan ta’addanci.
Aika aikar ‘yan bindiga akan hanyar Burkina Faso zuwa jamhuriyar Nijer ta fara jefa matafiya cikin halin zullumi ganin yadda wannan al’amari ke kara tsananta a tsakanin wadannan kasashe 2 makwabtan juna.
To amma masu sharhi akan sha’anin tsaro sun gargadi hukumomin akan bukatar matsa kaimi wajen tantance wadanda suka cancanci shiga aikin soja.
A Jamhuriyar Nijar ‘yan kasuwa sun yi barazanar rufe kasuwanni da shagunan kan titi a ranar alhamis mai zuwa.
Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta kwashe daruruwan ‘yan kasar da suka tare a kasar Senegal da sunan bara galibinsu mata da yara kanana wadanda suka sauka birnin Yamai a karshen mako kafin daga bisani a mayar da su garuruwansu na asali.
Hukumomin shari’a a jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar sallamar akasarin mutanen da suka kama a yayin zanga zangar watsi da sakamakon zaben da aka gudanar a kasar a farkon shekarar 2021 a yayin da a daya bangare ake ci gaba da daukan matakan inganta yanayin rayuwar fursinoni a gidajen yari.
Kungiyar Amnesty International ta bayyana damuwa game da halin kuncin da fursunoni ke ciki a gidan yarin Koutoukale na jihar Tilabery a Jamhuriyar Nijar,
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira tsadar kujerar hajji sakamakon yadda ejoji ke son cin kazamar riba a cewarta, zargin da tuni suka yi watsi da shi.
A jiya alhamis a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar Ministocin albarkatun ruwa daga kasashen yankin tafkin Chadi sun tantauna da kwararru akan hanyoyin farfado da harakokin yau da kullum a yankin mai fama da matsalolin tsaro.
A Jamhuriyar Nijar Hukumar kula da ayyukan dakon kaya daga tashoshin jiragen ruwa zuwa sassan kasar ta shirya wani taron horo ga masu dakon kaya da ‘yan kasuwar dake shigo da kaya daga waje ta yadda zasu lakanci dubarun da zasu basu damar cin moriyar wannan fanni fiye da yadda abin yake a yanzu.
‘Yan bindiga sun afka wa wata motar jigila mai dauke da fasinjoji sama da 40 akan hanyarsu ta zuwa birnin Yamai bayan da suka fito daga birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, cikinsu har da ‘yan sanda uku.
Kungiyar REJEA mai fafitikar samar da ruwan sha ta shirya wani taron hadin guiwa da gidauniyar Noor ta uwargidan shugaban kasa Hajiya Hadiza Bazoum da nufin tayar da hukumomi da masu hannu da shuni daga barci akan maganar samar da wadatar ruwan sha mai tsafta .
A yayin da hukumomin Nijer suka ayyana shirin gabatar wa majalisar dokokin kasa bukatar samun hadin kanta wajen girke dakarun rundunar Barkhane a kasar bayan ficewar rundunar daga Mali, kwamandan rundunar ta kasar Faransa ya ce kai tsaye zasu koma gida a maimakon zuwa wata kasar waje.
A jamhuriyar Nijer a karshen wani taron da ya hada sarakunan gargajiya, shugabaninn addinai, wakilan kungiyoyin cikin gida, na MDD, da na kungiyar EU don duba halin da ake ciki game da batun mutunta ‘yancin mata da yara kanana.
Shugabanin al’umar jihar Tilabery sun kira wani babban taron da zai hada rukunonin al’umar jihar a karshen makon nan domin yin nazarin mafitar matsalar tsaron da ta haddasa tsayawar al’amura, shekaru kusan 7 duk da irin matakan hadin gwiwar da gwamnatin Nijar da wasu kasashe aminai suka dauka.
Allah ya yi wa shugaban gidan Rediyo Amfani na jamhuriyar Nijer Alhaji Gremah Boukar rasuwa a yau talata 8 ga watan maris a wata asibitin birnin Tunis inda aka kwantar da shi yau makwanni 2.
Babban sakataren kungiyar kasashen Musulmi wato OIC ya kai ziyara Jamhuriyar Nijer a ci gaba da zagayen kasashen yankin tafkin Chadi da na Sahel da nufin bada gudunmowa wajen nemo bakin zaren game da matsalolin tsaro da na canjin yanayi da suka addabi jama’a.
Domin Kari