A jamhuriyar Nijer mutuwar wani soja cikin yanayin hazo a hannun wasu wadanda ba a san ko su waye ba ta haddasa cece kuce a tsakanin jama’a la wani lokacin da wasu rahotanni ke cewa hukumomi sun kadammar da kame kamen jami’an tsaro da farar hula.
Kungiyar CODDAE da hadin guiwar Cibiyar bunkasa ayyukan samar da makamashi a nahiyar Afrika (CESAO -AI ) sun shirya taro da nufin tattaro shawarwarin shugabanin kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin makamashi.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta cimma yarjejeniya da bankin duniya akan wani shirin samar da wutar lantarki da hasken rana wanda aka yi lakanin Haske Project da nufin inganta harkokin jama’a a birane da kuma karkara.
Jihar Diffa mai makwaftaka da jihohin Yobe da Borno a Najeriya ta bangaren kudu, na da iyaka da kasar Chadi ta bangaren gabas, yankin ya fada cikin matsalar tsaro a shekarar 2015
‘Yan kasuwa sun rufe shagunan ranar Laraba a birnin Yamai da nufin nuna kin amincewa da sabon tsarin karbar kudaden harajin da suke dauka a matsayin babbar barazana ga sha’anin kasuwanci a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki.
Shugabanin hukumomin shiga Tsakani daga kasashen yammacin Afrika mambobin kungiyar UEMOA sun fara gudanar da taro a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer domin duba gudunmuwar da zasu bayar wajen warware rigingimun da ake fama da su a kasashen yankin.
A yayinda shugaban kasar Nijer ke alfahari da sallamar wasu gaggan ‘yan ta’adda daga gidan yari a matsayin wata hanyar nemo bakin zaren tashin hankalin da ake fama da shi a wasu sassan kasar, masu rajin kare hakkin dan adam na bayyana ra’ayoyi mabambanta akan fa’ida da hallacin wannan yunkuri.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun kaddamar da wani Shirin bude cibiyoyin karatu domin daliban da matsalar tsaro ta yi sanadin rufe makarantun boko matakin da kungiyoyin malamai suka yaba da shi koda yake kuma sun gargadi mahukunta akan bukatar tsaurara matakan tsaro a irin wadannan cibiyoyi.
A yayinda gwamantin Jamhuriyar Nijer ta ayyana shirin gabatar da batun baiwa rundunar Takuba ta kasashen Turai da Barkhane ta kasar Faransa izinin girke dakarunsu a kasar bayan ficewa daga Mali wasu ‘yan Nijer na ganin shirya zaben raba gardama ita ce mafita.
Jamhuriyar Nijer, Najeriya da Algeria sun rattaba hannu akan yarjejeniyar farfado da aiyukan shimfida bututun iskar Gaz daga Najeriya zuwa Aljeriya ratsawa ta Nijer da nufin sayarda iskar gaz a kasuwanin kasashen nahiyar turai.
A wannan Juma’a ake kammala wannan taro da wata sanarwar karshen taro mai kunshe da shawarwarin da za a gabatarwa gwamnatocin kasashe mambobin CEDEAO.
A karshen wani taron da ya gudana jiya laraba a birnin Paris wanda ya sami halartar wasu shugabanin kasashen yammacin Afrika, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ayyana shirin kwashe sojojin rundunar Takuba da na rundunar Barkhane daga Mali.
A Jamhuriyar Nijar alkali mai shigar da kara a kotun birnin Yamai ya jaddada aniyar samar da haske a game da kisan wani dalibin sakandare da ya rasu bayan da wani jami’in tsaro ya bude wuta akan wata motar dalibai a ranar Talata.
Kungiyoyin dalibai a birnin na Yamai sun yi kira da a kauracewa ajujuwan karatu har sai an gudanar da kwakkwaran bincike.
A wani yunkurin daidaita al’amuran shara’a dai dai da zamanin da ake ciki a yau a duniya hukumomin jamhuriyar Nijer sun kaddamar da wani kwamiti mai alhakin nazarin gyaran fuskar kundin shara’ar kasar da kundin tsarin laifikan da aka gada daga mulkin mallakar Faransa.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta kaddamar da fasalin ayyukan agajin gaggawa domin wasu miliyoyin ‘yan kasar dake cikin matsanancin halin karancin cimaka da wadanda ke cikin halin bukatar abinci mai gina jiki sakamakon farin da aka yi fama da shi a damanar da ta gabata.
A jamhuriyar Nijer matasa daga jam’iyyu masu wakilcin majalisar dokokin kasa sun fara halartar wani taron horo da ke maida hankali akan irin rawar da ya kamata matasa su taka a fagen siyasa ta yadda za a samu wakilcin matasa sosai a al’amuran gudanar da mulki ko na shugabancin jama’a.
Shugaban kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross Peter Maurer ya gudanar da ziyara a jihohin Tilabery da Diffa don duba halin da jama’a ke ciki a wadanan yankuna masu fama da matsalolin tsaro da illolin canjin yanayi.
A jamhuriyar Nijer kananan ‘yan kasuwa sun bukaci hukumomin kasar su sake tunani a game da sabon tsarin biyan kudin harajin TVA da suka shimfida a farkon shekarar nan ta 2022.
Domin Kari