Noma Tushen Arziki
Kungiyar da ke rajin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya SERAP ta nemi gwamnatin tarayya ta janye jerin sunayen mutane shida da aka ce sune suka wawure dukiyar kasar.
Shugban Najeriya Muhmmadu Buhari ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar bikin Easter, inda ya yi kira ga ‘yan kasar da su yi amfani da lokacin bikin su kaunaci juna da kuma gujewa duk abubuwan da ka iya tayar da zaune tsaye.
Bayan umarnin da gwamnatin jihar Zamfara ta bayar na cewa a bindige duk wani da aka samu dauke da makamai ba bisa ka’ida ba, a yunkurin da take yi na dakile hare-haren 'yan bindiga, ‘yan bindigar yankin na cewa hakan ba zai samar da zaman lafiya ba a jihar.
Kiristoci a fadin duniya sun fara gudanar da bukukuwan Easter, domin tunawa da zagayowar ranar da aka gicce Yesu Almasihu, yayin da shugabannin addinai a Najeriya ke kira na musamman kan zaman lafiya da fahimtar juna.
Yayin da zaben shekarar 2019 ke karatowa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC na cewa ta dauki matakan hana duk wani magudi.
Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan lambar yabo ta bogi da ake cewa an baiwa shugaba Mohammadu Buhari.
Bayan tserewar mutanen da suka zargi Sanata Dino Melaye da saya masu makamai, 'yan sanda sun ayyana Sanata Melaye a matsayin mutumin da ake nema ruwa a jallo.
An kammala wani babban taron habaka harkokin kasuwanci da kudi na musulunci da aka gudanar tare da hadin gwiwar ma’aikatar kudi ta Najeriya, wanda kungiyar habaka masana’antu masu zaman kansu a nahiyar Afirka ta shirya a Legas.
Ciki da Gaskiya Wuka Bata Hudashi
Rahotanni daga Najeriya na cewa daliban makarantar Dapchi da kungiyar Boko Haram ta sace ta kuma sako su, sun koma gida bayan da aka kai su Abuja, babban birnin Najeriya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tarwatsa tawagar wasu matasa da suka fito kan tituna suna zanga-zanga don bayyana rashin jin dadinsu kan gazawar gwamnatin jihar, wajen kammala ayyukan wasu hanya.
Wata tawaggar jami’an ma’aikatar ilimi ta jihar Sokoto ta ziyarci daliban jihar da ke karatu a jami’ar Yamai don duba halin da suke ciki, a ci gaba da zagayen daliban da gwamnatin sokoto ta aika kasashen waje domin neman ilimi.
Rundunar sojan Najeriya ta Operation Lafiya Dole da ke aikin wanzar da zaman lafiya a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ta sake bude hanyar Maiduguri zuwa Bama, da ta hada zuwa garin Banki na jihar Borno.
Shugaban Najeriya Mohmmadu Buhari yayi ganawa ta musamman a fadar gwamnati da ‘yan matan Dapchi da iyayensu, inda ya bada tabbatacin cewa gwamnati zata kare sauran makarantu da kuma tabbatar da an inganta sha’anin ilimi a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Kungiyar lauyoyi a jamhuriyar Nijar na bikin cika shekaru 30 da kafuwa, hakan yasa lauyoyin ke amfani da wannan dama domin tantaunawa akan hanyoyin tabbatar da ‘yancin ma’aikatar shari’a a kasar.
Gwamnatin jihar Nasarawa tare da hadin gwiwar hukumar tsaro da kare al’umma ta ‘kasa Civil Defense, sun horas da matasa 5,900 kan yadda zasu samo bayanai daga al’umma don hana afkuwar tashin hankali tun kafin ya afku.
Mutumin da ake zargi da kai hare-haren bam a garin Austin dake jihar Texas ta Amurka, ya mutu ta hanyar tayar da bam a dai-dai lokacin da 'yan sanda suka tunkareshi.
Ministan watsa labaran Nijeriya ya ce yan ta’addar Boko Haram sun saki yan mata 101 cikin 110 da suka sace a Arewa maso gabashin Najeriya a garin Dapchi a watan da ya gabata.
Domin Kari