Ma’akatar lafiya ta jihar Kastina ta tabbatar da cewa mutane fiye da 300 ne suka kamu da cutar sankarau, kuma 30 sun mutu sanadiyyar cutar.
Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatarwa da Muryar Amurka cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun sako ‘yan matan Dapchi yau Laraba, amma kungiyar Amnesty International ta jaddada cewa dole sai an gudanar da bincike.
Mako guda bayan da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya ziyarci garin Dapchi, kungiyar Boko Haram ta maido da ‘yan matan sakandaren Dapchi da ta sace.
Noma Tushen Arziki
Malaman jami’ar Yamai sun ba da sanarwar kawo karshen yajin aikin da suka shafe wata guda suna gudanarwa da nufin nuna rashin jin dadi game da dukan da suke zargin wasu dalibai sun yi wa wani malamin jami’ar a tsakiyar watan jiya lokacin da wani sabani ya shiga tsakaninsu.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatin taryaya ta damu matuka da sace ‘yan matan Dapchi, sai dai masana na nuna damuwa kan rashin matakan tsaro tun kafin a sace ‘yan matan.
Alkalin babbar kotun tarayyar Najeriya Justice Gabriel Kolawale, ya janye daga wata shari’a da ta shafi tsohon mai bada shawara kan tsaro Kanal Sambo Dasuki.
Hukumar raya birane ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno sun bude wasu rukunin gidaje 300 a kauyen Ngwom da ke karamar hukumar Mafa a jihar.
A daidai lokacin da ake kokarin shawo kan tashe-tashen hankula da ke faruwa a wasu sassan jihar Taraba, batun da ake dangantawa da rikicin Makiyaya da manoma, yanzu haka kungiyoyin Fulani na zargin ana yi musu kamun dauki dai-dai ciki har da matan da ke zuwa sayar da nono a kasuwa.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC tace ba za ta amince da yadda gwamnatoci jihohi ke ci gaba da takura ‘yancin kananan hukumomi ba, kasancewa suma hukumomi ne masu zaman kansu bisa kundin tsarin mulkin kasar.
A dai dai lokacin da ake kokarin samo bakin zaren magance tashe-tashen hankulan dake faruwa a jihar Taraba, hukumomin tsaro a jihar sun gargadi al’ummomin da suka tara makamai da su gaggauta mika su ga hannun jami’an tsaro kafin lokaci ya kure.
A karon farko shugaban Najeriya Mohmmadu Buhari ya kai ziyara jihar Yobe, inda ya jaddada matsayar gwamnatinsa kan aikin da take yi na ganin an ceto ‘yan matan makarantar Dapchi.
Rundunar tsaro ta Operation Safe Haven a jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane 21 a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Zirsha da ke karamar hukumar Bassa.
Kwamiti na musamman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa domin tunkarar matsalolin shiyyar Arewa maso gabas a sanadiyar rikicin Boko Haram, ya gudanar da ayyukan kiwon lafiya na tsawon mako guda a jihar Gombe.
Hukumomin lafiya a jihar Jigawa da ke arewa maso yamamcin Najeriya, sun ce sama da mutane 50 ne suka kamu da cutar sankarau da kuma wasu cutuka na daban a jihar, kuma yanzu haka an tabbatar da mutuwar 14 daga cikinsu.
Kungiyoyin addinin Islama a Jamhuriyar Nijar sun yi kira ga bangarorin da ke ja in ja kan sabuwar dokar harajin kasar su zauna kan teburin sulhu don samar da zaman lafiya a kasar.
Hukumomi a jihar Zamfara sun tabbatar da mutuwar shugaban Fulani ‘yan bindiga da aka fi sani da Buharin Daji, wanda ke zama jigon rashin zaman lafiya ta hanyar kai hare-hare da satar shanu da kuma garkuwa da mutane a yankin.
Jami’an tsaro a jamhuriyar Nijar sun kama wasu mutane uku ‘yan asalin kasar Ghana, ‘dauke da makamai iri daban-daban.
Rundunar sojin saman Najeriya ta shirya taron bita na musamman ga ‘yan jaridar dake bada rahotannin tsaro a kasar, kan yadda zasu hada rahotannin tsaro tare da kaucewa haddasa fitina.
Domin Kari