Dan takarar Shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, jiya Litini, ya yi kiran da a kama dahir, game da manufofin harkokin waje na ruguza mayakan ISIS da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, a maimakon nemar sa kasashen waje su rungumi tsarin rayuwa irin na Amurka.