A fadar gwamnatin jihar Neja, Minna, an kafa dokar ta hana hawa babur daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safiya.
Yayin da yan gudun hijira a jihar Taraba ke ci gaba da kokawa kan rashin samun kayayyakin tallafi da gwamnatin tarayya ta turo jihar, biyo bayan takaddamar data kaure a tsakanin gwamnan jihar da kuma Ministan harkokin mata.
Gocewar kasa, wadda mahaukaciyar guguwa mai suna "Earl" ta haddasa, ta hallaka mutane 38 a yankin gabar Mexico da Caribean, a cewar jami'ai a jiya Lahadi.
A wannan makon da ya gabata, takaddamar shugabanci ta bullo a kungiyar nan mai tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram wadda ke Najeriya, al'amarin da wasu ke ganin alama ce cewa karshen kungiyar ya fara zuwa.
An dakatar da daukacin 'yan tawagar Rasha a gasar kasa da kasa ta Olympic na nakasassu, wadda za a yi a watan Satumba, a matsayin hukuncin da aka yanke ma kasar saboda amfani da kwayoyi masu kara kuzari.
Jiya Lahadi Shugaban Turkiyya Rajab Tayyib Erdowan, ya sha alwashin cigaba da yin fito-na-fito da duk wani mutum ko wata hukuma da ke nemar yin makarkashiya ga gwamnatinsa.
Hedkwatar tsaron Najeriya tace dakarun kasar zasu ci gaba da kai farmaki akan tsagerun Niger Delta a jihohin Lagos da Ogun.
Yanzu haka dai ‘yan siyasa na ci gaba da bayyana ra’ayinsu kan bukatar hukumomin binciken cin hanci da rashawa su fito da gaskiyar takaddamar zargin aringizon kudi ko cushe a Majalisar Wakilai kan kasafin kudin Najeriya na bana.
Rundunar Sojin Nigeria, ta tabbatar da cewa an kashe sojoji 11 tare da Hafsa ‘daya a lokacin rikicin sojojin da mutanen kauyen Kopa dake karamar hukumar Bosso a jihar Neja.
Kasar China ta yi shelar tanada hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifin kamun kifi (ko su) a ruwayen China, ciki har da wadanda ta ayyana a matsayin na ta a Tekun Kudancin China.
Shugaba Obama da Firaministan Singapore Lee Hsien Loong, sun jaddada aniyarsu ta kaddamar da 'yarjajjeniyar yankin Pacific ta Trans-Pacific mai cike da takaddama.
Caccakar da dan takarar shugaban kasar Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya ke sha, ta kara tsanani jiya Talata, saboda sukar wani iyalin Musulmin Amurka wadanda dan su ya mutu yayin da ya ke yaki ma Amurka a Iraki a 2004.
Hukumar kai dokin gaggawa ta kasa NEMA na jihar Adamawa ta yaye daliban firamare Dubu Daya da Dari Shida da Tamanin, a sansanoninta hudu da suka sami guraben karo ilimin a kwaleji daban-daban a fadin Najeriya.
Gwamnatin shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, tace ta na ci gaba da biyan tsofaffin ‘yan bindigar yankin Niger Delta alawus alawus din su, bayan wani tsaiko da aka samu na tsawon watanni hudu.
Shirin gwamnatin tarayya na gyara halayya da tunanin tsoffin ‘yan kungiyar Boko Haram, wanda sukayi watsi da akidar kungiyar suka mika makamansu ga gwamanati.
Jiya Litinin, cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka, ta gargadi mata masu juna biyu su guju kai ziyara wani yanki a jahar Florida, inda aka samu karin mutane da suka kamu da cutar Zika.
Wata tawagar wakilan majalisar dokoki na Turkiyya suna nan Washington domin matsin lamba kan bukatar da kasar ta gabatarwa hukumomi a Washington, na ganin an mika mata tsohon Limamin nan Fethullah Gulen, wanda kasar take zarginsa da kitsa yunkurin juyin mulkin nan da bai sami nasara ba.
A Syria, an harbe wani jirgi soja mai saukar ungulu a Arewa maso Yammacin kasar, dukkan mutane biyar da suke jirgin sun mutu.
Cacar baki tsakanin dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump da mahaifin wani sojan Amurka musulmi da dan kunar bakin wake ya kashe a Iraqi a 2004, shine ya mamaye yakin neman zaben shugabancin Amurka a jiya Litinin.
Rundunar sojojin ruwan Najeriya ta rugurguza wasu haramtattun matatun Mai na tsagerun Niger Delta.
Domin Kari