Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai Associated Press ya fitar ranar Litinin na nuni da cewa, dakarun kasar Sudan ta Kudu sun yiwa ma’aikatan jinkai fyaden taron dangi, suka yi ta lakada masu duka, suka kuma yi masu fashi, musamman ma’aikatan jinkai Amurkawa a wani otel dake birnin Juba ranar 11 ga watan Yuli.