Adadin wadanda su ka mutu a wata fashewar bam a birnin Aden mai tashar jirgin ruwa a kasar Yemen, ya cigaba da karuwa, yayin da masu ayyukan ceto su ka yi tono baraguzan wata cibiyar horar da sojoji, wandda ake kyautata zaton dan kunar bakin wajen ISIS ne ya yi rugu-rugu da ita.