Tsohon Firai Ministan Birtaniya David Cameron ya bada sanarwar yin murabus daga kujerarsa ta majalisar dokoki, abin da zai kawo karshen harkokin siyasarsa, makwanni bayan da ya sha kasa a zaben raba gardama na ranar 23 ga watan Yuni na neman zama ko ficewar kasar daga kungiyar Taryyar Turai.
Kimanin Alhazai miliyan Biyu ne sukayi tsayuwan Arfa a wajen birnin makka, a matsayin wani babban ginshikin aikin hajji da musulmi ke gudanarwa duk shekara.
Kungiyar Adamawa Peace Initiative mai hankoron wanzar da zaman lafiya a yankin Adamawa, tayi wani taro a daya daga cikin dakunan taro na Majalisar Dokokin Amurka, inda ta bayyana cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a ayyukanta.
A yau Litinin ne ministan tsaro na Koriya ta Kudu ya yi gargadin cewa Koriya ta Arewa zata iya sake yin wani gwajin makamin Nukiliya a kowanne lokaci.
Rigima ta kaure a kasar Turkiyya tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga a Kudu maso Gabashin Turkiyya, bayan da gwamnati ta fitar da sanarwar cewa ta maye gurbin wasu zabebbun kantomomi da shugabannin kananan hukumomi har 28, a wasu garuruwan Kurdawa.
Kasar Pakistan ta yi watsi da wani kiran da Afghanistan ta yi na neman a barta ta soma gudanar da hidimar cinikayya ta kai tsaye tsakaninta da India, ta hanyar barin ita Afghanistan, wacce bata da tekuna, ta ci gaba da anfani da hanyoyin da suka ratsa ta cikin Pakistan, kamar yadda aka shata a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Pakistan din da Afghanistan.
'Yar takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar democrats ta Amurka, Hilary Clinto, ba zata yi kyamfen yau Litinin ko gobe Talata ba a jihar California bayanda likitoci suka tabattarda cewa tana fama da ciyon harakari.
‘Yan Sanda a Faransa sun tarwatsa wata makarkashiyar kai wani mummunan harin ta’addanci a birnin Paris a kwanaki biyu da suka gabata, inda suka kame wani matashi mai shekaru 15, da ake zarginsa da shirya harin ta’addanci.
Daya daga cikin Amurkawa yan sama jannati da wasu yan Rasha biyu sun sauko lamin lafiya a Kazakhstan da safiyar Laraba bayan da suka kwashe watanni shida suna gudanar da ayyuka a sararin samaniya.
Fada tsakanin dakarun gwamnatin kasar Syria da mayaka a lardin Hama ya tilasta kimanin mutane dubu dari kauracewa gidajensu tsakanin ishirin da takwas ga watan Agusta zuwa biyar ga watan Satumba, bisa ga cewar hukumar ayyukan jinkai ta MDD.
Kananan manoma a jihar Adamawa sun zargi ma’aikatar noma da kwadai ta musu su fadada gonakinsu bisa alkawarin zata samar da rancen noma karkashin tsarin bunkasa ayukan noma na shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari da aka lakabawa Anchor Borrowers Scheme amma daga baya ta rage yawan kadada da adadi kudin zata ranta masu kan kowace kadada.
Amurka ta zargi Rasha da tura jiragen yaki kusa da wani jirgin leken asirin Amurka kan tekun Baharum jiya Laraba, abin da jami’an sojin Amurka suka ce yana da hadari kuma bai kyautu ga kwararru ba, yayin da Moscow ke cewa, ta kiyaye dokokin kasa da kasa na zirga-zirgar jirage a cikin sararin samaniya.
Tsoffin ma’aikata ‘yan fensho dake jihohin Arewa maso Gabas, sunce suna bin gwamnatocinsu kudaden fensho da garatuti fiye da Naira Miliyan Dubu Dari.
‘Yar takarar shugabancin Amurka ta jam’iyar Democrat Hillary Clinton tace, abu mafi muhimmanci ga kowane shugaban kasa shine ya kasance mai natsuwa. Yayinda abokin hamayyarta na jam’iyar Republican Donald Trump yace, kada irin halinsa da tunaninsa su dami masu kada kuri'a.
Yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke fara haramar shirye-shiryen sallar Laiya, yanzu haka farashin Raguna na kara tashin gwauron zabi, haka kuma jama’ar Najeriya na cigaba da kokawa game da matsatsin rayuwa.
Hukumar Abinci Ta MDD, ta raba kayan abincin da ake matukar bukatarsu ga 'yan Iraqi sama da 30,000 a birnin Qayyarah da kewaye da ke Arewacin Iraki, mai tazarar kilomita 60 kudu da birnin Mosul.
Da kakkausan harshe Amurka ta yi Allah wadai da munanan hare-hare na baya-bayan nan da aka kai birnin Kabul, da su ka kashe tare da raunata dinbin jami'an tsaro da farar hula, yayin da ta ke kuma baiwa Afghanistan tabbacin cewa za ta hada kai da ita don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da kuma cigaban kasar.
Domin Kari