An bude taron Majalisar Dinkin Duniya zagaye na Saba’in da Daya, inda shugabannin kasashe daban daban daga fadin duniya ke halartar taron, ciki harda shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari.
Mutumin da ake kyautata zato shine ya tada da bam a daren Asabar a birnin New York da ya ranauta mutane 29, ya fara samun sauki a asibiti daga raunin harsashi bayan harbi da yan sanda suka yi mashi.
Majalisar Wakilan Najeriya zata dawo zama bayan hutun mako Takwas da duba batun Aringizo a kasafin Kudin Bana.
Asusun bunkasa ayyuka da koyar da sana’o’i ga ‘yan Najeriya da ake kira Industrial Training Fund ko kujma ITF a takaice, ya koyar da kuma horas da wasu dalibai har 1,100 da aka koya musu sana’o’in hannu daban daban a garin Maiduguri.
Ministan kyautata rayuwar mata da kula da jin dadin jama’a na tarayyar Najeriya Hajiya A’ishatu Jummai Alhassan, ta ce babu gaskiya a korafe-korafen cin zarafi da gallazawa mata da yara mata a sansanonin ‘yan gudun hijira na jihohin Arewa maso Gabashin kasar.
Ma’aikatar kasuwanci da zuba jari a Saudiyya tace an kwace tare da lalata gurbatattun abinci da kuma ‘karin wasu sinadaran sarrafa abincin a birnin Makka da Madina da Ta’if.
An kashe wani babban hafsan sojin Somalia a wani harin bam na cikin mota a Mogadishu, babban birnin kasar a jiya Lahadi.
Akalla mutane 20 aka hallaka a kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a cewar wani jami’i a jiya Lahadi.
An gano cewa mutumin da ya soke mutane tara a wata kasuwar zamani ta jihar Minnesota dake arewacin kasar Amurka wani Ba’amurke ne amma dan asalin a kasar Somalia.
Magajin Garin birnin New York Bill de Blasio yace yakamata mutane su saurara su samu cikkakken bayani game da tsahin wani bam a daren Asabar a unguwar Manhattan wanda yayi raunata mutane 29.
Rahotanni a Najeriya na nuni da cewar a kowacce rana akan sare itatuwa kimanin Miliyan Daya da Dubu Dari Biyar domin yin makamashi.
Shugaban kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya a jihar Adamawa, ya bayyana farin cikin su game da masalaha da aka samu a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya da kuma gwamnatin jihar game da albashinsu da suka dake basu samu ba.
A jamhuriyar Nijar kotu ta sallami wasu ‘yan adawa su kimanin 6 cikinsu har da dan Majalisar dokokin ‘kasar Sumana Sanda, jigo a jam’iyyar MODEN LUMANA bayand a suka shafe watanni sama da 10 a gidan yari saboda zarginsu da yunkurin shirya tarzoma ta hanyar amfani da makami zargin da ‘yan adawa suka sha musantawa.
Kaddamar da rigakafin cutar Shan inna a dukkan yankunan Arewacin Najeriya idan aka ‘dauke jihar Kwara, na gudana ne ta hanyar ‘daukar matakan kula da zirga zirgar yara ta kan iyakokin kasar.
Ana Saura kimanin makwanni biyu shekarar kudi ta zo karshe, kungiyoyi masu tallafawa yan gudun hijira a nan Amurka suna cikin tsakiyar abin da ake kyautata zaton zai zama kwararrar baki mafi girma a cikin sama da shekaru goma, biyo bayan yunkurin shigo da Karin masu gudun hijira da yakin basasa a Syria da IS ta raba da muhallansu.
Kotun duniya tace zata fara mayar da hankali a kan laifukan da suka shafi lalata muhalli, da masu yiwa albarkatun kasa illa, da kuma samun filaye a kan hanyoyin da basu dace ba.
Shugaban Ghana John Dramani Mahama na jami’iyar National Democratic Congress mai mulki da dan takarar babban jami’iyar adawa ta New Patriotic Party Nana Addo Dankwa Akufo-Addo da wasu yan takarar shugaban kasar sun karbi takardun shiga takara daga hukumar zaben kasar don shiga zabe ranar 7 ga watan Disamba. Masu takarar zuwa majalisa suma sun fara karbar takardunsu na shiga takara.
Babban jami’in diplomaisiya na kasar Philippines ya gargadi Amurka a kan jan hankalin gwamnatinsa a kan hakkokin bil adama, abin da ya sa kakakin fadar White House ya yi kira ga dukkan kasashe, musamman kawayen Amurka da su mutunta hakkokin bil Adama.
Wasu wakilan majalisar dokokin Birtaniya sun kushewa matakin da Birtaniya da kuma Faransa suka dauka a shekara ta Dubu Biyu da Goma sha Daya da ya kai ga kifar da gwamnatin shugaban Libya Moammar Gaddafi.
A Jamhuriyar Nijar karamin Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Ayyukan jin kai a kasashen yankin Kudu da Sahara, Toby Lanzer, ya kai wata ziyara a kasar wanda ya samu ganawa da al'ummar Diffa dake fama da matsalar tsaro.
Domin Kari